Bayan Daka Ya Yi Daka, Ministan Tinubu Ya Ba Ƴan Najeriya Hakuri, Ya Fadi Shirinsu

Bayan Daka Ya Yi Daka, Ministan Tinubu Ya Ba Ƴan Najeriya Hakuri, Ya Fadi Shirinsu

  • Yayin da ake cikin wani hali a Najeriya, Ministan kasafi da tsare-tsare, Atiku Bagudu ya fito fili ya ba ƴan kasar hakuri
  • Sanata Bagudu ya ce tabbas ana cikin wani a kasar suna ba da hakuri amma fa daukar matakan sun zama dole ne
  • Ministan ya bayyana haka ne a yau Laraba 22 ga watan Mayu inda ya ce Bola Tinubu ya dauki hanyar gyara kasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Ministan kasafi da tsare-tsare, Atiku Bagudu ya ba ƴan Najeriya hakuri kan halin kunci da ake ciki.

Atiku Bagudu ya bayyana haka ne a yau Laraba 22 ga watan Mayu yayin taron Ministoci a birnin Tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

"Da wahala", Jigon APC ya gaji da kame kamen Tinubu wajen gyara Najeriya kamar Lagos

Ministan Tinubu ya ba da hakuri kan halin da ake ciki
Ministan kasafi, Atiku Bagudu ya ba ƴan Najeriya hakuri. Hoto: Sen. Atiku Abubakar Bagudu.
Asali: Facebook

Bagudu ya kare matakan Tinubu a Najeriya

Duk da ba da hakuri da ya yi, Ministan ya kare matakan da Bola Tinubu ke dauka da cewa za su inganta Najeriya, cewar Leadership.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ministan ya ce daukar matakan da shugaban ya yi sun zama dole domin tabbatar da inganta tattalin arzikin kasar, Tribune ta tattaro.

"Ina ba da hakuri kan halin kunci da aka shiga saboda matakan da ake dauka, amma hakan ya zama dole ne."
"Tabbas muna da yakinin cewa tsare-tsarenmu suna kan hanya, amma dole sai ana auna su lokaci bayan lokaci."

- Atiku Bagudu

Bagudu ya fadi alfanun matakan Tinubu

Sanata Bagudu ya ce akwai matakan da dole za a dauka domin jawo hankulan masu zuba hannun jari.

Ya ce hakan shi zai kawo karin kudin shiga a kasar wanda za a inganta ilimi da walwalar jama'a da kuma dakile matsalar tsaro.

Kara karanta wannan

Lauyoyin Murja sun yi fatali da ita, sun fadi nadamar da suka yi a shari'arta

Wannan martani na Ministan na zuwa ne yayin da ƴan Najeriya ke kokawa kan halin matsin rayuwa da kunci da suke ciki.

Bagudu ya saba kare tsare-tsaren Tinubu

A wani labarin, kun ji cewa, Ministan kasafi a Najeriya, Atiku Bagudu ya ce Bola Tinubu ya dauki matakai masu kyau domin inganta tattalin arzikin Najeriya.

Tsohon gwamnan na Kebbi ya ce abin da Tinubu ya yi ya nuna jarumta wanda ya kamata gwamnatocin baya su yi domin inganta Najeriya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel