"Yadda Tinubu Ya Bi Ya Hana Tattalin Arzikin Najeriya Durkushewa", Kashim Shettima

"Yadda Tinubu Ya Bi Ya Hana Tattalin Arzikin Najeriya Durkushewa", Kashim Shettima

  • Gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta bayyana cewa dole ta dauki tsauraran matakai domin ceto tattalin arzikin Najeriya daga durkushewa baki daya
  • Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ne ya sanar da hakan a taron bikin cika wannan gwamnatin shekara ɗaya tana jagorantar 'yan Najeriya
  • Kashim Shettima ya ce idan 'yan kasar nan sun yi hakuri za a bi dadi sosai na gaba saboda matakan cire tallafin fetur da ake kuka da shi zai taimaki kowa

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Abuja-Gwamnatin tarayyar Najeriya ta bayyana cewa tsauraran matakan da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta bijiro da su ne suka ceto tattalin arzikin kasar daga durkushewa.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Kwanaki bayan samun mukami, tsohon Gwamna ya kare Tinubu

Mataimakin Shugaban kasa, Kashim Shettima ne ya bayyana haka yayin taron duba ci gaban da Bola Tinubu ya samu a shekarar farko a matsayin shugaban Najeriya.

Kashim Shettima
Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya bayyana matakan da suke dauka ne ke ceto tattalin arzikin kasa Hoto: Kashim Shettima
Asali: Facebook

The Nation ta tattaro cewa Alhaji Kashim Shettima ya jaddada cewa duk da wahalar da ake sha a yanzu, kasar nan na kan turbar samun wadatar arziki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa, dole ce ta sa Bola Tinubu daukar matakan da yanzu ‘yan Najeriya ke kuka da su, domin ta haka ne kawai za a samu wadata a nan gaba.

‘Za a warwasa’ Inji Kashim Shettima

Mataimakin shugaban kasar nan, Kashim Shettima ya jaddada cewa matakan da gwamnatinsu ke bijiro da su za su kawo gagarumin sauyi ta fuskar tattalin arziki.

Ripples Nigeria ta wallafa cewa ‘yan Najeriya, ‘ya’yansu da jikokinsu za su warwasa a shekaru masu zuwa a cewar Shettima.

Kara karanta wannan

"Gwamnatin Bola Tinubu ta jefa Najeriya cikin tsaka mai wuya," Dattijon Arewa

A kalamansa:

“An fara haka ne ta fuskar cire tallafin man fetur. An dauki matakin ne domin ceto kasar nan daga bashin da ya fi karfinta wanda kuma ya ke ci gaba da karuwa a shekarun baya.”

Ya yi albishir da cewa kudrorin gwamnatin tarayya guda takwas za su zakulo kasar nan daga halin da take ciki zuwa matakin da kowa zai ji dadi.

‘Ana shan wahala,’ Dattijon Arewa

A baya mun kawo muku labarin cewa daya daga 'yan kungiyar dattawan Arewa, Farfesa Usman Yusuf ya caccaki yadda gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ke tafiyar da kasar nan.

Farfesan ya bayyana cewa matakan da gwamnatin tarayya ta dauka ne suka jefa Najeriya a cikin mawuyacin halin da ake ciki a yau.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Online view pixel