"Yana Hawa Najeriya Ta Durkushe": Tsohon Sakataren Gwamnatin Buhari Ya Soki Tinubu

"Yana Hawa Najeriya Ta Durkushe": Tsohon Sakataren Gwamnatin Buhari Ya Soki Tinubu

  • Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya a mukin Muhammadu Buhari, Babachir Lawal ya soki salon mulkin Bola Tinubu
  • Babachir ya ce rantsar da Tinubu ke da wuya Najeriya ta durkushe ba tare bata lokaci ba bayan sanar da cire tallafin mai a kasar
  • Jigon APC ya ce yanzu komai ya lalace a kasar inda ya koka kan yadda kudin sufuri ya ninka har sau uku a Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Injiniya Babachir Lawal ya yi magani kan kamun ludayin gwamnatin Bola Tinubu.

Babachir ya ce tun bayan hawan Tinubu karagar mulkin Najeriya kasar ta ruguje ta rasa madafa.

Kara karanta wannan

Dan majalisar PDP ya nemi Tinubu ya fara tafiye tafiye a mota ko ya hau jirgin haya

Na hannun daman Buhari ya caccaki salon mulkin Tinubu
Babachir Lawal ya soki salon mulkin Tinubu bayan Buhari ya sauka. Hoto: @metasedecor, @Imranmuhdz.
Asali: Twitter

Babachir ya fadi babban kuskuren Tinubu

Tsohon sakataren ya ce cire tallafin mai shi ne babban kuskuren da Tinubu ya yi tun kafin nadin mukamai a gwamnatin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Na hannun daman tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya bayyana haka yayin hira da gidan talabijin na Trust.

Har ila yau, Babachir ya ce sanar da cire tallafin shi ne ya jefa jama'ar kasar cikin mummunan yanayi da har yanzu suke ciki.

Babachir ya koka kan farashin sufuri

Lawal ya ce matakin ya shafi harkokin sufuri wanda shi ne ginshikin tattalin arziki da talaka da mai kudi ke tunkaho da shi.

"Zan sake maimaita abin da dade da fada, kazo ka gwamnati a ranar da aka rantsar da kai ka dauki mummunan mataki."
"A lokacin ba shi da Ministan tsare-tsare da zai tsara yadda za a samar da mafita idan aka cire tallafin mai."

Kara karanta wannan

Yayin da ake kukan tsadar kujerar hajji, Tinubu ya tausaya da tallafin biliyoyi

"Kuma ba kada Ministan kudi ko masu baka shawara kuma babu wadanda za su ce ta dace a yi ko kuma sabanin haka."

- Babachir Lawal

Babachir ya koka kan yadda kudin sufuri ya ninka har sau uku yayin da yake kokarin dauko wasu kayan gona daga Zaria.

Majalisar Dinkin Duniya ta yabawa Tinubu

A wani labarin, Majalisar Dinkin Duniya ta yaba da salon mulkin Shugaba Bola Tinubu a Najeriya kan matakan da ya ke dauka.

Majalisar ta ce shugaban ya yi namijin kokari wurin inganta tattalin arzikin Najeriya da kuma dakile matsalolin tsaro a ƙasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel