Tapswap Ya Fadi Dalilin Matsalar da Ƴan Najeriya Ke Fuskanta a Dangwale, Ya Ba da Haƙuri

Tapswap Ya Fadi Dalilin Matsalar da Ƴan Najeriya Ke Fuskanta a Dangwale, Ya Ba da Haƙuri

  • Yayin da ƴan Najeriya ke fuskantar matsala a Tapswap, kamfanin ya yi martani kan matsalar da ta yi ƙamari
  • Ƴan kasar suna ci gaba da kokawa kan yadda suka gagara shiga manhajar Tapswap cikin kwanakin nan
  • Legit Hausa ta tattauna da wani masanin 'Kirifto' kan matsalar da ake samu musamman game da Tapswap

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Kamfanin Tapswap ya magantu yayin da yan Najeriya ke samun cikas a kokarin neman sulalla a manhajarsa.

Wannan na zuwa ne yayin da yan kasar ke kokawa kan dakile su da aka yi wurin daddana Tapswap din.

Kamfanin Tapswap ya ba ƴan Najeriya hakuri kan matsalar da suka fuskanta
Tapswap ya yi martani kan jita-jitar cewa ya dakile ƴan Najeriya. Hoto: Getty Images/Tim Roberts and X/Tapswap. An yi amfani da hotunan ne kawai domin misali.
Asali: UGC

Tapswap ya musanta cire ƴan Najeriya

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kamfanin ya fitar a shafin X a yau Juma'a 24 ga watan Mayu.

Kara karanta wannan

Sarautar Kano: Abba Kabir ya magantu kan sahihancin samun takarda daga kotu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamfanin Tapswap ya ce babu wani shiri na cire ƴan Najeriya daga tsarin inda ya ce an samu wasu matsalolin na'ura ne.

"Ya ku ƴan Najeriya, muna sane da matsalar da kuke fuskanta wajen shiga Tapswap saboda wasu matsaloli."
"Dole muka fara tantance wasu yankuna da aka samu matsala, kamar yadda muka yi alkawari zamu shawo kan matsalar."
"Muna godiya da dukkan mambobinmu da ke fadin duniya, muna maraba da ku da kuma godiya da hakuri da goyon baya da kuke bamu."

- Tapswap

Ƴan Najeriya sun nemo wata hanyar dangwale

Duk da haka wasu yan Najeriya suna amfani da hanyar da bata dace ba domin samun damar dangwale tare da samun sulalla.

Sai dai masana na ganin yin amfani da VPN hatsari ne ga duk mai amfani da wata hanya ta hakar sulalla.

Legit Hausa ta tattauna da wani masanin 'Kirifto' kan matsalar da ake samu musamman game da Tapswap.

Kara karanta wannan

Ministar Tinubu ta ji wuta, ta ba da tulin kyaututtuka ga ƴan mata 100 da za a aurar

Muhammad Aliyu Zubair ya ce daman an tabbatar da cewa tantance mutane suke yi saboda tsaron manhajarsu.

Sai dai wasu mutane suna kuskure wurin amfani da VPN wanda zai iya jawo musu matsala daga baya musamman bayan kammala dangwalen.

"Muna yawan gargadin mutane da amfani da VPN da kuma 'Auto Clicker' a harkoki irin wannan saboda hatsari ne."
"Tun a baya idan ba a mantaba 'Satoshi' suna gargadi kan shiga manhajarsu da VPN wanda ke musu barazana."

- Muhammad Zubair

Ƴan Najeriya sun gagara dangwale a Tapswap

A wani labarin, kun ji cewa cikin 'yan kwanakin, yawancin 'yan Najeriya da ke harkar hakar ma'adanan Taspwap sun kasa samun damar shiga manhajar da ke kan Telegram.

Idan ba a manta ba, a baya mun ruwaito yadda wata matashiya ta kwantarwa 'yan Najeriya hankali kan wannan matsalar, yayin da TapSwap ya ce yana kan yin gyara.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel