Matsin tattalin arziki
Bola Ahmed Tinubu da gwamnatinsa za su yi kokarin karfafa darajar Naira. Tope Fasua ya ce nan gaba Dalar Amurka za ta iya saukowa zuwa N600 ko N500.
Duk da jigo ne shi a jam'iyyar PDP, Ben Murray Bruce ya ce tattalin arzikin Najeriya ya fara bunkasa bayan karya darajar Naira bayan Muhammadu Buhari ya sauka.
Dele Alake ya ce za a kafa jami’an tsaron da za su rika yakar barayin ma’adanai domin a inganta kudin shiga kuma a magance ta’adin ‘yan bindiga a Najeriya.
Muhammadu Buhari ya damka mulki ana bin Najeriya bashin kimanin Naira Tiriliyan 87.4bn, yanzu Bola Tinubu ya na shirye-shiryen cin wasu bashi daga kasashen waje.
A karshen makon nan aka ji labari Dala ta na karyewa a kasuwar canji tun da babban bankin Najeriya ya fara sallamar bankuna bashin kudin waje da su ke bi.
Bola Tinubu ya fadi inda Najeriya za ta koma samun kudin shiga a maimakon fetur, za a yaki masu hako ma’adanai a boye, sannan za a kawo tsare-tsaren saukaka harkar.
Ministan kasafin kudi da tsare-tsare, Sanata Atiku Abubakar Bagudu ya yi bayanin yadda gwamnatin tarayya za ta batar da karin N2.18tr nan da zuwa karshen shekara.
Za a iya samun saukin farashin kayan kasashen waje idan aka tafi a haka. Yanzu ‘yan kasuwar canji su na saye da saida kowace Dalar Amurka tsakanin N1100 zuwa N1200
Babban malamin addini ya bayyana bukatar a daina amfani da sabbin Naira da aka kawo a zamanin shugaban kasa Muhammadu Buhari na a shekarar nan da ake ciki.
Matsin tattalin arziki
Samu kari