Yanzu Yanzu: Babu Ranar Daina Amfani da Tsofaffin N200, N500 da N1000 Inji CBN

Yanzu Yanzu: Babu Ranar Daina Amfani da Tsofaffin N200, N500 da N1000 Inji CBN

  • Sabuwar sanarwa ta fito daga bankin CBN cewa ba za a daina karbar tsofaffin Nairori a matsayin halatattun takardun kudi ba
  • Isa Abdul Mumin ya shaida cewa ba a ji dadi ba da aka yi kokarin canza manyan kudi, saboda haka babu maganar daina a karbarsu
  • Har bayan Disamban 2023, mutum zai iya zuwa banki ya bada tsofaffin N200, N500, N1000 ko kuwa bankin CBN ya karbesu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

FCT, Abuja - Babban banki watau CBN ya tabbatar da cewa tsofaffin N200, N500 da kuma N1000 za su cigaba da zama kudi a Najeriya.

Punch ta rahoto bankin ya na sanar da al’umma cewa an tsawaita wa’adin amfani da N200, N500 da N1000 da aka yi yunkurin canzawa.

Kara karanta wannan

Babu Kudi: Takardun Nairori sun fara gagarar mutane a gari, duk da matakin CBN

Sababbin Nairori
Sababbin kudin da aka buga bayan canza Naira Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Babban bankin ya sake ya tsawaita wa’adin halaccin kudin da aka canza a bana ya ce suna nan a matsayin kudi har illa Ma shaa Allahu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar CBN a kan tsofaffin Nairori

Darektan sadarwa na bankin Isa Abdul Mumin ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar.

An yi wa sanarwar da aka fitar a yammacin Talata da taken “CBN zai bar tsofaffin Nairori a matsayin halattattun kudi har sai baba-ta-gani.”

Isa Abdul Mumin ya ce an dauki wannan mataki ne lura da yadda ake yi a duk duniya.

Jami’in ya kara da cewa yunkurin canjin kudin da bankin CBN ya yi a baya ya zo da wahala, saboda haka ne za a gujewa maimatuwar hakan.

"N200, N500, N1000 suna nan a kudi" - CBN

"Duk wasu kudi da babban bankin Najeriya ya bada kamar yadda sashe na 20 (5) na dokar dokar CBN ya yi tanadi, zai cigaba da zama kudin kashewa, har sai baba-ta-gani, har bayan wa’adin farko na 31 ga watan Disamba 2023.

Kara karanta wannan

Sojin saman Najeriya sun yi ruwan bama-bamai kan motocin 'yan ta'adda a Borno

Babban bankin kasar ya na aiki da hukumomin da su ka dace domin janye umarnin kotu a kan batun.
Saboda haka, rassan bankin CBN a fadin kasar nan za su cigaba da badawa da karbar duka takardun kudi, tsofaffin da sababbi, daga kuma zuwa ga bankunan kasuwa.

- Dr. Isa Abdul Mumin

Shawarar da bankin CBN ya bada

A karshen sanarwar, an yi kira ga al’umma su yi hattara wajen kula da kudin kasar saboda ganin an tsawaita lafiyar takardun Nairorin.

Sannan an bukaci mutane su rungumi kafofin ciniki na zamani domin cinikin yau da kullum yayin da ake kukan karancin takardu a yau.

Naira ta tashi, ta sauko a BDC

‘Yan kwanaki kadan bayan an yi ta murnar tashin Naira, sai ga rahotanni da ke nuna cewa abubuwa sun sake tabarbarewa a kasar nan.

Tsakanin N1050/$1 zuwa N1120/$1 ‘yan kasuwar canji su ka rika saidawa mutane Dala bayan hobbasar da kudin gidan ya yi a kasuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel