Gwamnatin Bola Tinubu Za Ta Kirkiro Sababbin ‘Yan Sanda Domin Gadin Ma’adanai

Gwamnatin Bola Tinubu Za Ta Kirkiro Sababbin ‘Yan Sanda Domin Gadin Ma’adanai

  • Gwamnatin tarayya ta ce za ta kafa wata runduna da aikinta kurum shi ne yaki da wadanda ke hakar ma’adanai a sace
  • Dele Alake ya ce magana ta yin isa a kan wannan shiri, kuma shugaba Bola Tinubu ya na goyon bayan yunkurin nan
  • Ministan yake cewa za ayi haka ne saboda a inganta kudin shiga kuma a magance ta’adin ‘yan bindiga a Najeriya

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Gwamnatin tarayya ta bayyana shirinta na kirkiro wasu dakaru na musamman da za a ba nauyin yakar masu satar ma’adanai.

Ministan cigaban ma’adanai na kasa, Dele Alake ya shaida wannan da aka yi wata hira da shi a gidan talabijin NTA a karshen makon jiya.

Kara karanta wannan

Matsala ta kunno, mata ta auri mijin da ba ya haihuwa cikin rashin sani, zamansu ya yi tsami

Mr. Dele Alake ya ce za a kafa wadannan jami’an tsaro ne domin gwamnatin tarayya ta samu karin kudin shiga sosai a bangaren ma’adanai.

Bola Tinubu
Alake ya ce Gwamnatin Tinubu za ta tsare ma'adanai Hoto: @Dolusegun
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ma'adanai: Akwai matsalar tsaro - Alake

A yayin da yake amsa tambayoyi a game da kalubalen da su ke fuskanta a bangarensa, Alake ya nuna daga ciki akwai matsalar tsaro.

Rahoton ya ce saboda a magance rashin tsaron ne za a hada-kai da sauran jami’an tsaron kasar kuma a kirkiro wasu dakaru na musamman.

"Bayanan sirri da mu ka samu sun nuna wasu masu hakar ma’adanai ta bayan-fage su na da dangataka kai-tsaye da ta’adin ‘yan bindiga a bangarorin Najeriya da yawa.
Shiyasa na ke aiki da hukumomin jami’an tsaro da-dama da Mai ba shugaban kasa shawara kan tsaro, za a kafa jami’an tsaro kuma shugaban kasa ya na goyon baya.

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP da kujerarsa ke tangal-tangal ya nemi afuwar talakawan jiharsa kan abu 1 da ya faru

Za mu kirkiro dakarun ‘yan sanda na musamman. Za mu kira su ‘yan sandan ma’adanai."

- Dele Alake

Aikin da jami'an tsaro za su rika yi

Idan an samar da rundunar, aikinsu ba zai tsaya a fannin ma’adanai kurum ba, za su rika amfani wajen magance tsaro har a cikin teku.

Alake ya ke cewa ma’aikatar cigaban ma’adanai za ta kula da jami’an idan an kafa su, duk saboda ganin an rgae damuwa da arzikin fetur.

Minista zai yi da gaske a aikinsa

Ganin Bola Tinubu ya taso Ministoci da duk wanda aka ba mukami a gaba, za a rika bibiyar aikinsa, Festus Keyamo SAN ya zage dantsensa.

Ana da labari Ministan harkokin jiragen saman ya fadawa na karkashinsa tsere ne da za a ga wanda zai kubuta, kuma ba zai bari a kore shi ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel