Naira Ta Farfado a Kasuwar Canji, Akwai Yiwuwar Dala Ta Karye Kwanan Nan

Naira Ta Farfado a Kasuwar Canji, Akwai Yiwuwar Dala Ta Karye Kwanan Nan

  • Bayan an shafe kwana da kwanaki Dalar Amurka ta na tashi a kasuwa, yanzu darajar Naira ta fara farfadowa a Najeriya
  • Daga kan fiye da N1300, a yanzu ‘yan kasuwar canji su na saye da saida kowace Dalar Amurka tsakanin N1100 zuwa N1200
  • Wasu sun rika sayen kudin kasar Amurkan su na boye da niyyar farashinta zai tashi, hakan ya rika karya kimar kudin gida

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja – Bayan makonni ta na karyewa, a ranar Litinin dinnan, Naira ta cigaba da tashi a kasuwar BDC ta ‘yan canjin kudin ketare.

The Cable ta ce an yi cinikin Dala a kan N1, 150 a farkon makon nan, hakan ya nuna darajar kudin Najeriya ta karu da akalla N80 kenan.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya ware wa INEC naira biliyan 18 na zabukan gwamnonin jihohi 3

A ranar Juma’ar da ta gabata, ‘yan kasuwa sun saida Dala guda a kan N1230, hakan ya nuna Dala ta karye da 6.5%, kuma ta na kara fadi.

Naira
Bankin CBN ya jawo Dala ta sauka Hoto: @Cenbank
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Yan canji sun samu saukin Dala

Wani ‘dan canji ya shaidawa jaridar wahalar da Dala ta yi ya ragu sosai a yanzu. Watakila shi ne karon farko tun tashin Naira a Agusta.

‘Yan kasuwa su na sayar da kudin kasar Amurkan a kan N1,120 bayan sun saye ta a kan N1,150, masu harkar canjin su na cin ribar N30.

“Dala ta na dawowa kasuwa sannu a hankali. Yanzu mu na ganin Dalar Amurka sosai.”

- Wani 'dan kasuwa

Farashin Dala ya sauka a I& E

Darajar da Naira ta kara ya kai 5.68% daga karshen makon jiya zuwa farkon makon nan a bankuna da kafar I & E na babban bankin CBN.

Kara karanta wannan

Jami'an NDLEA sun kame tan 6 na ganyen maye a jihohin Najeriya shida 5, bayanai sun fito

A ranar Alhamis, bankuna sun saidawa abokan huldarsu Dala a N837.49, zuwa Juma’a sai aka ji farashin kudin ya gangaro zuwa N789.94.

Bayanan da aka samu daga FMDQ OTC Securities Exchange sun nuna sai da aka yi ciniki a kan N900/$ kafin darajar Dala ta dawo N696.06.

Legit ta fahimci darajar Naira ta na karuwa a halin yanzu, ana hasashen cewa zuwa Disamba, $1 ba za ta wuce N750 a kasuwar BDC ba.

Sabon gwamnan bankin CBN ya na cigaba da kokarin ganin an samu karin Daloli a kasa.

An samu canjin hannu a bankin CBN

A watan Satumba aka samu labari Mai girma Bola Ahmed Tinubu ya amince da nadin Olayemi Michael Cardoso ya zama Gwamnan CBN.

Shugaban kasar ya kuma nada mataimakan gwamnoni hudu da za su taya shi aiki, daga ciki akwai Muhammad Sani Abdullahi watau Dattijo.

Asali: Legit.ng

Online view pixel