Shugaban Kasar Malawi Chakwera Ya Haramtawa Kansa Da Ministocinsa Fita Waje

Shugaban Kasar Malawi Chakwera Ya Haramtawa Kansa Da Ministocinsa Fita Waje

  • Gwamnatin kasar Mawali ta yanke hukuncin dakatar da shugaban kasa da mukarrabansa daga duk wasu tafiye-tafiye zuwa kasashen waje
  • Haka zalika, ya bayyana matakan rage tafiye-tafiyen cikin gida ga ma'aikatan fadar shugaban kasar, tare da rage darajar kudin kasar na Kwacha
  • Gwamnatin, ta dauki wannan matakin ne biyo bayan fama da matsalar tattalin arziki da ya haifar da karancin man fetur, da karin farashin abinci a kasar

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Kasar Malawi - Shugaban kasar Malawi, Lazarus Chakwera, ya dakatar da duk wasu tafiye-tafiye zuwa kasashen waje da ya shafi jami'an gwamnati.

Wannan matakin, ya shafi duk mukarraban gwamnatinsa, ciki har da shi kansa da ministocinsa, har zuwa karshen wannan shekara, a wani mataki na tsuke bakin lalitar kasar.

Kara karanta wannan

Almundahanar N200m: Gwamnatin Filato ta fara bincikar tsofaffin ma'aikatan hukumar alhazai

Fadar shugaban kasar Malawi
Shugaba kasar yan dauki matakin daina fita kasashen waje don tsuke lalitar kasar, a wani yunkuri na farfado da tattalin arziki Hoto: opc.gov.mw
Asali: Twitter

A wani jawabi kai tsaye da ya gabatar a gidan talabijin a daren Laraba, Chakwera ya umarci dukkanin ministocin da ke kasashen waje da su koma gida, jaridar The Cable ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Malawi ta zabtare kudaden man fetur na ministoci da jami'an gwamnati

Haka zalika, ya bayyana matakan rage tafiye-tafiyen cikin gida ga ma'aikatan fadar shugaban kasar.

Matakan za su yi aiki har zuwa watan Maris, 2024, inda ya ke cewa:

"Duk wata tafiya da ta zama dole wani mukarrabi na ya y, to ya zama dole ne a gabatar da bukatar hakan ga ofishina don samun izini na".
"Na ba da umarnin a zabtare duk wasu kudade na sayen fetur ga ababen hawan ministoci, manyan sakatarorin gwamnati, daraktoci da duk membobin manyan hukumomin gwamnati."

Rahoton jaridar TRT Africa ya yi nuni kan yadda kasar Malawi ke fama da matsalar tattalin arziki da ya haifar da karancin man fetur, da karin farashin abinci da kuma karancin kudaden waje.

Kara karanta wannan

Rahoto: Ɗangote zai siyar da katafaren jirgin alfarma da ya siya don murnar ranar haihuwarsa

Malawi ta rage darajar Kwacha

A makon da ya gabata ne babban bankin kasar ya sanar da rage darajar kudin kasar na kwacha zuwa dala daya kan kwacha 30.

Wannan dai shi ne karo na biyu da kasar Malawi ke karya darajar kudinta, bayan da ta fara yin hakan a watan Mayun shekarar 2022 don farfado da kudaden ajiyarta a kasashen waje.

Kasashe 10 da suka fi talauci a nahiyar Afirka

Legit Hausa ta kawo maku wani rahoto, kan wasu kasashe goma da suka fi talauci a Afirka kamar yadda kididigar bankin duniya tayi a shekarar 2018.

Malawi itace kasa ta biyu mafi talauci a Afirka saboda matsalolin da kasar ke fama dashi cikin shekarun da suka gabata.

Al'umma kasar na fama da karancin asibitoci da makarantu. Yawancinsu manoma ne sai dai suna fama da rashin lafiya daban-daban.

Asali: Legit.ng

Online view pixel