Naira Ta Gama Zabure-zabure a Kasuwa, Ta Koma Gidan Jiya da $1 ta Harba N1120

Naira Ta Gama Zabure-zabure a Kasuwa, Ta Koma Gidan Jiya da $1 ta Harba N1120

  • Sannu a hankali kuma ana cigaba da rububin kudin kasashen waje a BDC, Dalar Amurka ta cigaba da tashi a kasuwar canjin
  • A makon jiya, kudin Najeriya ya kara daraja bayan wani yunkuri da CBN ya yi na biyan tsohon bashin da bankuna su ke bin sa
  • Ba a je ko ina ba sai aka ji mutane sun cigaba da sayen kowace Dalar kasar Amurka a kan abin da ya zarce N1, 000 a BDC

Abuja - Kudin Najeriya na Naira ya na cigaba da gangara a sahun kudin duniya, yanzu ana sayen Dala a kan fiye da N1, 000.

Rahoton da The Cable ta fitar a tsakiyar makon nan ya ce sai mutum ya bada N1, 120 kafin ya iya samun duk Dalar Amurka guda.

Kara karanta wannan

A shirya: Fadar Shugaban Kasa ta fadi mamayar da Tinubu zai yi wa 'yan boye dala

Fadin da darajar Naira ta yi a ranar Talata ya kai 9.27% ko kuma a ce kudin Najeriyan ya rasa N95 na kimarsa a cikin sa’o’i 24.

Naira
Dala na wahalar da Naira Hoto: www.reuters.com
Asali: UGC

Naira ta fadi a kasuwar BDC

Wasu ‘yan kasuwa da ke harkar canji sun saye Dala a kan N1, 100 sannan su ka saida ta a N1, 120, an ci ribar N20 a duk guda.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

‘Yan Bureau De Change (BDC) da aka fi sani da ‘yan canji sun bayyana cewa a halin yanzu ana yawan neman kudin ketaren.

Hakan na zuwa ne bayan Naira ta yi kwararran tashi a kasuwar canji a makon jiya, har ana tunani farkon fadin Dala kenan.

'Yan boye Dala na cin kazamar riba

A makon jiya an yi ta hasashen cewa lokaci ya yi da Naira za ta tashi, ana ba masu boye Dala shawarar saida abin hannunsu.

Kara karanta wannan

Barayi sun sacewa Najeriya man fiye da Naira Tiriliyan 4.3 a shekaru 5 Inji NEITI

Kafin a je ko ina kuma sai aka ji labarin ya canza, kudin kasashen wajen da ake da su a kasuwa ba su iya biyan bukatar jama’a ba.

Dala ta koma N860 a I & E

A kafar I & E na masu kasuwancin kasa da kasa, kudin gidan ya karye da 7.53%, Nairametics ce Naira ta rasa N60.89 a kan $1.

A maimakon N809.02 da aka saida Dala a ranar Litinin, jiya sai da $1 ta koma N869.91, a haka ne aka ji wasu su na yabon bankin CBN.

Bayanan da aka samu daga FMDQ Securities Exchange sun nuna mafi tsadan farashin da aka saida Dala a jiya shi ne a kan N1, 100.

Naira za ta ba masu boye Dala mamaki

Labari ya zo a makon nan cewa Mai ba shugaban kasa shawara kan harkar tattalin arziki ya aikawa masu boye Daloli sakon gargadi.

Kara karanta wannan

Ga mari, ga tsinka jaka: APC ta yi wa Peter Obi raddi kan batun shari’ar zaben 2023

Nan gaba Dalar Amurka za ta fadi raga-raga, Dr. Tope Fasua ya na ganin $1 sai ta koma kusan N500 saboda tsare-tsaren da za a kawo.

Asali: Legit.ng

Online view pixel