Matsin tattalin arziki
Gwamnati na kokarin hana Dala cigaba da tashin kullum-yaumin. Dalar Amurka ta dade da haura N1000 a kasuwar canji, Edun ya shaida cewa ana fama da karancin kudi.
A game da tsarin da aka kawo, za a gane ba dole ba ne abinci ya yi sauki ko Dala ta yi araha, babu tabbacin farashin shinkafa za ta sauko nan gaba kadan.
CBN ya dauko tsarin kudi wanda ya sha bam-bam da na lokacin Muhammadu Buhari. Wani masanin tattalin arziki ya fada mana akwai rashin hikima a lamarin Bola Tinubu.
‘Yan fansho da tsofaffin sojojin da su ka dade da ritaya za su samu kudin da za a raba. Gidaje miliyan biyar za su samu N25, 000 a Oktoba, Nuwamba da Disamba.
Yadda ake kukan tashin man fetur, haka komai ya tashi, Man Jet A1 ko ATF da ake amfani da su a jiragen sama sun yi tsada, ‘yan kasuwa su na sayen lita a kan N1000
Akwai talakawan da ke karkashin tsarin CCT wanda za a rika aika masu N5000. Gwamnatin tarayya ta ci bashin $800m daga bankin Duniya domin rage radadi.
Duk da Bola Tinubu ya yi alkawarin zai gyara tattalin arziki, an canza Dala a kan sama da N1, 100. Naira ta yi lalacewar da ba a taba gani ba a tarihin Najeriya
Dr. Ifeanyi Okeke ya zama sabon shugaban hukumar SON. Kafin nan Shugaban kasa ya tsige shugabannin hukumomin CAC, ITF, NEPC, OGFZA, NSDC, ya nada masu sababbi.
Gwamnan CBN zai soke canjin kudi, eNaira da wasu canji da Muhammadu Buhari ya kawo. Olayemi Micheal Cardoso ba zai biyewa kashe kudi domin noman shinkafa ba.
Matsin tattalin arziki
Samu kari