A Bar Batun Man Fetur, Tinubu Ya Fadi Inda Najeriya Za Ta Koma Samun Kudin Shiga

A Bar Batun Man Fetur, Tinubu Ya Fadi Inda Najeriya Za Ta Koma Samun Kudin Shiga

  • Bola Ahmed Tinubu ya nuna gwamnatinsa za ta karkato da akalarta ga bangaren ma’adanai domin a samu kudin shiga da kyau
  • Kamar yadda man fetur ya kawowa Najeriya makudan kudi, sabon shugaban kasar ya na so a samu arziki sosai da ma’adanai
  • Gwamnatin Tinubu za ta dage domin ganin bayan duk masu hako ma’adanai a boye, sannan a kawo tsare-tsaren saukaka harkar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abuja - Bola Ahmed Tinubu ya ce gwamnatin da ya ke jagoranta ta na kokarin ganin ma’adanai sun zama mafi girman hanyan samun kudin shiga.

Mai girma Bola Ahmed Tinubu ya yi wannan bayani ne a ranar Talata a wajen taron AFNIS da aka shirya a Abuja, Vanguard ta fitar da rahoton a jiya.

Shugaban Najeriyan ya samu wakilcin Sakataren gwamnatin tarayya, George Akume a wannan taro da ya gudana a babban dakin taron ICC a Abuja.

Kara karanta wannan

Tinubu: Duk minista ko wani da ba zai iya tabuka komai ba, ya tafi ya ba ni wuri

Shugaban Najeriya Tinubu
Bola Tinubu ya ce za a kauda kai daga fetur Hoto: @DOlusegun
Asali: Twitter

Tinubu: Ma'adanai za su zama sabon fetur

Kamar yadda Najeriya ta yi arziki da man fetur, Sanata George Akume ya ce za a iya yin hakan da ma’adanan da Ubangiji ya azurta kasar nan da su.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnatin Bola Tinubu ta ce a shirye ta ke da hada-kai da ire-irenta masu sha’awar kawowa al’umma cigaba wajen ganin arziki ya wadata mutane.

Gwamnatinmu za ta farkar da ma’adani daga barcin da su ke yi, domin taka muhimmiyar rawa wajen farfado da tattalin arziki, samawa mutanenmu ayyuka , inganta kudin shigan gwamnati da kuma kafa bangaren da duniya za ta yi sha'awa.
‘Yan Najeriya sun bada mamaki sun yi haka da bangaren mai. Man fetur ya zama mafi girman hanyar samun kudin shiganmu.
Za mu yi haka da bangaren ma’adanai, da kyawu kuma cikin hikima domin mun koyi darasi.

Kara karanta wannan

Ana shigowa babu Gayyata, Shugaban Kasa ya takaita taron FEC ga jami’an Gwamnati 4

- Bola Tinubu

Hattara ga masu hako ma'adanan haram

This Day ta ce shugaba Tinubu ya ja-kunne ga masu hako ma’adanai ta barauniyar hanya, ya ce za su gamu da fushin gwamnati na saba doka.

Baya ga narkon, Tinubu ya ce za su saukaka yadda ake kasuwanci, saboda wannan gyaran ne ya ce ya zabi Dr Oladele Alake ya zama Minista.

Bambancin Tinubu da Buhari a mulki

Adebayo Shittu wanda ya yi Minista daga 2015 - 2019 ya na cewa idan Muhammadu Buhari ya ba mutum aiki, ba zai taba tambaya a kan shi ba.

An rahoto tsohon ministan ya ce a gwamnatin Buhari, idan ba ka je ka neme shi ba, watakila sai ayi shekaru hudu bai waiwaye labarinka ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel