Kin Bayyanar Yahaya Bello a Kotu Ya Fusata Alkali, an Sake Ba EFCC Damar Kama Shi

Kin Bayyanar Yahaya Bello a Kotu Ya Fusata Alkali, an Sake Ba EFCC Damar Kama Shi

  • Shari'ar Yahaya Bello da hukumar EFCC na ci gaba da daukar sabon salo yayin da kotu ta jaddada umarnin kamo tsohon gwamnan
  • Tun da fari, Yahaya Bello ya roki babbar kotun tarayya da ke Abuja da ta hana EFCC ta kama shi; said dai kotun ta yi fatali da bukatar
  • Alkalin kotun, Mai shari’a Emeka Nwite, ya soki Yahaya Bello kan kin bayyana a gabansa duk da tarin sammacin da aka aika masa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta ki amincewa da bukatar janye umarnin kama Yahaya Bello, tsohon gwamnan jihar Kogi.

Kotu ta yi fatali da wata bukata da Yahaya Bello ya gabatar
Kotu ta jaddada umarnin kama Yahaya Bello, EFCC ta sake samun dama. Hoto: @officialEFCC
Asali: Facebook

Alkalin kotun Emeka Nwite, ya soki Yahaya Bello da gabatar da bukatar janye umarnin alhalin ya ki bayyana a gaban kotun, jaridar The Cable ta ruwaito.

Kara karanta wannan

A karshe, Tsohon Gwamna Yahaya Bello Zai Gurfana a Gaban Babbar Kotu a Abuja

Ya bayyana abin da tsohon gwamnan ya yi a matsayin wani yunkuri na kawo cikas ga karar da hukumar EFCC ta shigar a kansa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kotu ta daina sauraron Yahaya Bello

Mai shari’a Nwite ya dage cewa dole ne tsohon gwamnan ya zo kotu ya amsa zarge-zargen da EFCC ke yi masa a kan karkatar da akalla Naira biliyan 80.

Channels TV ta ruwaito alkalin ya ce tunda Yahaya Bello ya ki bin umarnin kotun, ba za a bari ya kara shigar da wata kara ba kuma ba za a saurare shi ba.

Alkalin ya kara da cewa ko da ace ba a bi ka'ida ba a wajen bayar da umarnin kama shi, to da ya kamata ne ya bayyana a gaban kotun domin kalubalantar hakan.

Yahaya Bello ya gabatar da wata bukatar

Kara karanta wannan

Rayuwa za ta yi sauki kuma abinci zai wadata a mulkina, Tinubu ya dauki alkawari

Bello yana kuma rokon kotun da ta dakatar da sauraron karar da EFCC ta shigar a kansa har sai kotun daukaka kara ta yanke hukunci kan makamanciyar wannan karar.

Ta bakin lauyansa, Abdulwahab Mohammed, tsohon gwamnan ya sanar da kotun cewa EFCC ta samu umarnin kotun daukaka kara da na ta dakatar da tuhumarsa.

Don haka lauyan ya ce tun da kotun daukaka kara ta sanya ranar 20 ga watan Mayu domin sauraron karar, ya kama babbar kotun tarayyar ta jira sakamakon karar kafin ta ci gaba da sauraron nata shari’ar.

Kotu ta ba da belin Hadi Sirika

A wani labarin, mun ruwaito maku cewa wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta ba da belin tsohon ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika, diyarsa da wasu mutane biyu.

An ruwaito cewa kotun ta bayar da belin Sirika da mutanen uku ne a kan Naira miliyan 100 kowanne tare da gabatar da mutane biyu-biyu da za su karbi belinsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel