Tsohon Gwamnan Kogi, Yahaya Bello Ya Yi Rashin Nasara a Babbar Kotun Tarayya

Tsohon Gwamnan Kogi, Yahaya Bello Ya Yi Rashin Nasara a Babbar Kotun Tarayya

  • Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya yi rashin nasara a yunkurin dakatar da shari'ar da ake masa kan badakalar N80bn
  • Babbar kotun tarayya mai zama a Abuja ta yi watsi da bukatar tsohon gwamnan saboda bai halarci zaman shari'a ba ranar Jumu'a
  • Alkalin kotun ya caccaki Yahaya Bello da lauyansa kan rashin zuwan wanda ake tuhuma, ya ce EFCC hukuma ce mai bin doka da oda

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Babbar kotun tarayya mai zama a Abuja ta yi watsi da buƙatar tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello a zamanta na ranar Jumu'a.

Alkalin kotun mai shari'a Emeka Nwite ya yi fatali da buƙatar tsohon gwamnan wanda ya nemi a dakatar da shari'ar da ake masa kan badaƙalar N80bn.

Kara karanta wannan

Matakai 5 da Gwamnatin Tinubu ta dauka da suka jefa ‘yan Najeriya a wahalar rayuwa

Yahaya Bello.
Tsohon gwamnan Kogi. Yahaya Bello ya yi rashin nasara a kokarin dakatar shari'arsa Hoto: Alhaji Yahaya Bello
Asali: Facebook

Bello ya bukaci alkalin ya dakatar da sauraron shari’ar da ake yi masa, bisa dalilin karar da hukumar yaki da masu yi wa tattalin arziki ta'adi (EFCC) ta shigar kan zargin cin mutuncin shugabanta, Ola Olukoyede.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kotu ta watsar da buƙatar Yahaya Bello

Da yake yanke hukunci kan wannan buƙata mai shari'a Nwite ya ce kotu ba za ta saurari batun ba har sai wanda ake ƙara ya gurfana a gabanta, Premium Times ta ruwaito.

"Ba za a saurari buƙatar ba har sai wanda ake tuhuma ya halarci zaman kotu, amma tun da wanda ake ƙara baya nan, ƙorafin ba zai karɓu ba."

Da yake sukar Yahaya Bello da lauyansa, alkalin ya ce tsohon gwamnan na kokarin bata tsarin shari’a ne ya hanyar ƙin gabatar da kansa a gaban ƙotu.

"Kai ne kake zuga wanda ake tuhuma, menene abin da kuke tsoro? Mutum nawa kuka taɓa jin an ce hukumar EFCC ta kashe? EFCC hukuma ce mai bin doka sau da ƙafa."

Kara karanta wannan

A karshe, Tsohon Gwamna Yahaya Bello Zai Gurfana a Gaban Babbar Kotu a Abuja

"Shin wanda ka ke karewa ne kaɗai tsohon gwamnan da EFCC ta gayyata? Ka kawo shi kotu, ni kuma zan saurari buƙatarka,” in ji alkalin.

Yahaya Bello zai gurfana a kotu

Biyo bayan kin dakatar da shari’ar da kotu ta yi, Mista Bello ya yi alkawarin mika kansa domin gurfanar da shi a gaban kuliya.

Lauyan tsohon gwamnan, Abdulwahab Mohammed, ya dauki nauyin gabatar da wanda yake karewa a gaban kotu a ranar 13 ga watan Yuni, The Cable ta ruwaito.

Fubara ya canza wurin zaman majalisa

A wani rahoton na daban yayin da rikicin jihar Ribas ke ƙara tsananta, Gwamna Fubara ya canza wurin zaman majalisar dokokin jihar Ribas.

A wata takarda mai ɗauke da kwanan watan 14 ga Disamba, 2023, gwamnan ya ce an ɗauke matakin ne saboda babu tsaro a zauren majalisar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262