A Karshe, Tsohon Gwamna Yahaya Bello Zai Gurfana a Gaban Babbar Kotun Tarayya a Abuja

A Karshe, Tsohon Gwamna Yahaya Bello Zai Gurfana a Gaban Babbar Kotun Tarayya a Abuja

  • Tsohon gwamnan Kogi, Alhaji Yahaya Bello ya amince zai gurfana a gaban babbar kotun tarayya mai zama a Abuja a watan Yuni, 2024
  • Lauyan Bello ne ya bayyana haka ga Mai shari'a Emeka Nwite bayan samun tabbacin EFCC ba za ta saɓa wa tanadin doka ba
  • Sakamakon rashin jayayya daga lauyan EFCC, mai shari'a Nwite ya ɗage zaman zuwa ranar 13 ga watan Yuni mai zuwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - A karshe tsohon gwamnan jihar Kogi, Alhaji Yahaya Bello ya amince ya mika kansa ga babbar kotun tarayya da ke zama a birnin tarayya Abuja.

Yahaya Bello ya amince zai miƙa kansa a gurfanar da shi a gaban kotun ramar 13 ga watan Yuni bisa tuhume-tuhumen da EFCC ta shigar a kansa.

Kara karanta wannan

Kin bayyanar Yahaya Bello a kotu ya fusata alkali, an sake ba EFCC damar kama shi

Tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Bello.
Yahaya Bello ya shirya gurfana a gaban kotu kan tuhume-tuhume da EFCC ke masa Hoto: Alhaji Yahaya Bello, OfficialEFCC
Asali: Twitter

Yahaya Bello ya sallamawa EFCC

A rahoton Leadership, lauyan tsohon gwamnan, Abdulwahab Mohammed ne ya bayyana hakan ga mai shari’a Emeka Nwite na babbar kotun tarayya a zaman ranar Juma’a.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mohammed ya ce tsohon gwamnan baya tsoron a gurfanar da shi, sai dai yana fargabar lafiyarsa idan ya shiga hannun hukumar yaƙi dacin hanci da rashawa EFCC.

Lauyan Yahaya Bello ya ci gaba da shaida wa kotun cewa, rayuwar wanda yake karewa na fuskantar barazana a Abuja, bisa haka ya yanke shawarar ɓuya.

Alƙali ya buƙaci Yahaya Bello ya gurfana

Mai shari’a Nwite ya sanar da yarjejeniyar cewa Bello zai miƙa kansa ga kotu, yana mai jaddada cewa EFCC ba za ta yi wani abu da ya saba wa tanadin doka ba.

Alkalin ya ce Bello ba shi ne tsohon gwamna na farko da hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta gayyata ba kuma ba zai zama na karshe ba, The Nation ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Tsohon minista Hadi Sirika ya kafa misali da annabawa yayin da ya gurfana a gaban kotu

Nwite ya ƙara da cewa a yanzu tuhumarsa kawai ake kan laifukan da ba a tabbatar ba, kuma doka tana ɗaukar wanda ake tuhuma a matsayin mara laifi har sai an tabbatar da laifinsa.

Yahaya Bello zai gurfana a kotu

Da yake martani kan jawaban alƙalin, Lauyan Yahaya Bello ya ce tun da sun samu tabbacin EFCC ba zata masa komai ba, tsohon gwamnan zai halarci zaman kotun.

"Daman abin da wanda nake karewa ke buƙata shi ne ya samu tabbacin tsaron lafiyarsa wanda ya jima cikin barazana na tsawon lokaci a Abuja," in ji shi.

Daga nan lauyan ya buƙaci a ba shi makonni huɗu domin ya zo da Yahaya Bello zaman kotu.

Bayan haka ne kuma alkalin ya sanya ranar 13 ga watan Yuni domin tsohon gwamnan ya gurfana a gabansa saboda lauyan EFCC bai yi jayayya ba.

Kotu ta ce a kamo Yahaya Bello

Kara karanta wannan

An zargi wani jami'in KEDCO da kashe abokinsa saboda abin duniya

A wani rahoton kuma shari'ar Yahaya Bello da hukumar EFCC na ci gaba da daukar sabon salo yayin da kotu ta jaddada umarnin kamo tsohon gwamnan.

Tun da fari, Yahaya Bello ya roki babbar kotun tarayya da ke Abuja da ta hana EFCC ta kama shi; said dai kotun ta yi fatali da bukatar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel