Kotu Ta Ba da Belin Tsohon Minista Hadi Sirika da Ɗiyarsa, an Kafa Sharuda

Kotu Ta Ba da Belin Tsohon Minista Hadi Sirika da Ɗiyarsa, an Kafa Sharuda

  • Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bayar da belin tsohon ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika da wasu mutane uku
  • Wadanda EFCC ta gurfanar tare da Sirika sun hada da diyarsa, Fatima; Jalal Hamma da kamfanin Al-Duraq Investment Ltd
  • Sirika, wanda ya yi aiki a gwamnatin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya gurfana gaban kuliya kan tuhume-tuhume shida

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bayar da belin tsohon ministan sufurin jiragen sama Hadi Sirika, ɗiyarsa, da wasu mutane biyu.

Hadi Sirika ya gurfana gaban kotu kan tuhume-tuhume 6
Kotu ta bayar da belin Hadi Sirika da wasu mutane 3 kan N100m kowanne. Hoto: @TosinOlugbenga
Asali: Twitter

Kotu ta ba da belin Hadi Sirika

Kotun ta ba da belin kowanne mutum daya a kan kudi Naira miliyan 100 kuma za su gabatar da mutum biyu-biyu da za su tsaya masu, Channels TV ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Yaki da ta'addanci: Ma'aikatar tsaro ta rabawa sojoji sababbin motocin yaki masu sulke

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar kotun, dole ne ya zamana wadanda za su tsaya masu sun mallaki kadarori a Abuja tare da kuma zama ‘yan kasa na-gari.

Waɗanda za su tsayawa wadanda ake karar za su gabatar takardar shaidar kadarori da dukkanin abubuwan da kotun take bukata.

EFCC na tuhumar Hadi Sirika

Mun ruwaito maku cewar hukumar EFCC ce ta gurfanar da tsohon ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika a gaban mai shari’a Sylvanus Oriji na babbar kotun.

An gurfanar da Sirika, wanda ya yi aiki a gwamnatin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari a gaban kuliya bisa tuhume-tuhume shida da aka yi wa kwaskwarima.

Daga cikin wadanda EFCC ta gurfanar tare da Sirika akwai diyarsa, Fatima; Jalal Hamma da kamfanin Al-Duraq Investment Ltd, bisa zargin cin zarafin ofis.

A cewar takardar tuhumar da gidan Talabijin na Channels ya gani, Sirika ya yi amfani da mukaminsa na Minista wajen bada haramtacciyar takwangila ga diyarsa da surukansa.

Kara karanta wannan

"Daukar fetur a jarka zai iya babbake fasinjoji," FRSC ta gargadi masu abubuwan hawa

EFCC ta tsare Hadi Sirika

Tun da fari, Legit Hausa ta ruwaito cewa hukumar EFCC ta tsare Hadi Sirika, tsohon ministan sufurin jiragen sama kan zargin zambar kudi ta sama da Naira biliyan takwas.

EFCC ta gudanar da bincike kan zargin rashawa da bayar da haramtattun kwangiloli ga diyarsa, 'yan uwansa da abokan huldarsa tare da karkatar da makudan kudade.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel