Hukumar EFCC
Shugaban hukumar EFCC, Olanipekun Olukoyede ya yi tone-tone kan yadda ya kaucewa yunkurin wasu yan siyasa da ke neman ba shi cin hanci yayin jana'izar mahaifiyarsa.
Kotun tarayya ta ba da belin Farfesa Usman Yusuf bayan gurfanar da shi da hukumar EFCC ta yi. EFCC ta zargi tsohon shugaban NHIS da almundahanar kudi.
Jami'an EFCC sun mamaye kotu da makamai, sun takaita shiga. Shaidu sun ce sunan Yahaya Bello bai bayyana a takardun kadarori ba. Kotu ta dage shari'ar.
Tsohon shugaban inshora ta NHIS ya ce hukumar EFCC sun kama shi kamar sun kama Bello Turji. Ya fadi yadda ya zauna a wajen EFCC da zama a kurkukun Kuje.
Bayan zaman babbar kotun Abuja, fitacciyar yar gwagwarmayar nan, Naja'atu Mohammed da Salomon Dalung sun nuna ɓacin ransu kan kama Farfesa Usman Yusuf.
Yayin da ake tuhumar tsohon shugaban hukumar inshorar lafiya ta NHIS, Babbar kotun Abuja ta ki amincewa da ba da belin Farfesa Usman Yusuf kan badakalar kudi.
An bayar da belin tsohon Minista, Kabiru Turaki, SAN, akan N1m bayan zarginsa da auren karya, lalata, da barazana. An dage shari’ar zuwa 11 ga Maris.
Kungiyar NCA ta bukaci hukumar EFCC ta kama tsohon gwamnan Kaduna, Nasir Ahmed El-Rufa'i cikin sa'o'i 72. NCA ta ce za ta yi zanga zanga a fadin Arewa.
Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El Rufa'i ya yi zargin gwamnati mai ci a jiharsa da siyasantar da binciken rashawa da ake yi wa wasu daga cikin jami'an gwamnatinsa.
Hukumar EFCC
Samu kari