Ba Kamar Tinubu ba, Atiku Ya Kawo Sabon Tsari a Yakin Neman Zabensa
- Phrank Shaibu ya bayyana shirin tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, kan yakin neman zabensa
- Shaibu ya bayyana cewa yakin neman zaben ba zai tsaya ga manyan biranen jihohi da gangamin siyasa kawai ba
- Ya ce matsin tattalin arziki da yunwa matsaloli ne da suka shafi ’yan Najeriya a ko’ina, ba tare da la’akari da yankin da suke zaune ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Daraktan Sadarwa da Dabarun Yada Labarai na Kwamitin Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa na jam’iyyar ADC, Phrank Shaibu, ya yi magana kan Atiku Abubakar.
Phrank Shaibu ya ce Atiku Abubakar zai gudanar da yakin neman zabensa a dukkan jihohin Najeriya 36 gabanin babban zaben 2027.

Source: Facebook
Shaibu ya bayyana hakan ne yayin wata hira da tashar Arise News a ranar Lahadi, 25 ga watan Oktoban 2026 inda ya yi watsi da fargabar cewa Atiku zai fi mayar da hankali kan jihohin arewacin Najeriya.
Ya ce jam’iyyar za ta fitar da jadawalin yakin neman zaben nan ba da jimawa ba, yana mai jaddada cewa babu jihar da za a bari a baya wajen ganawa da masu zabe.
A cewarsa, jadawalin zai bai wa jama’a damar ganin wuraren da Atiku zai ziyarta da kuma tantance yadda zai gudanar da yakin neman zabensa.
Atiku zai kamfe a kauyuka
Shaibu ya bayyana cewa shirin Atiku ba zai takaita ga gangamin siyasa a manyan biranen jihohi ba. Maimakon haka, za a gudanar da tarukan tattaunawa da jama’a, ziyartar al’umma da kuma kai ziyara kananan hukumomi da kauyuka.
Ya ce Atiku na bukatar ganawa da ’yan Najeriya kai tsaye domin sauraron matsalolin da suke fuskanta da kuma fahimtar bukatunsu.
Shaibu ya jaddada cewa yakin neman zaben zai ba tsohon mataimakin shugaban kasar damar mu’amala da masu zabe, maimakon dogaro kawai da manyan tarukan siyasa.
Ya kuma yi ikirarin cewa jama’a na fama da matsin rayuwa, don haka ya kamata ’yan siyasa su saurari koke-kokensu tare da fahimtar halin da suke ciki.

Kara karanta wannan
Tinubu na ganin ƴan adawa suka jefa ƙasa a halin ƙunci duk da matakan da ya ɗauka
Shaibu ya yi misali da matsalar yunwa
Daraktan ya ce matsin tattalin arziki da yunwa sun zama matsalolin kasa baki daya, wadanda za su iya yin tasiri kan yadda ’yan Najeriya za su zabi shugabanninsu a 2027.
A cewarsa, matsalolin da mutum ke fuskanta a Zamfara ba su bambanta da wadanda wani ke fuskanta a Legas idan batun yunwa da tsadar rayuwa ake magana a kai.
Bambanci da shirin yakin neman zaben Tinubu
Bayanin Shaibu ya zo ne a daidai lokacin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayyana shirin takaita halartar gangamin yakin neman zaben jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da kansa zuwa jihohi 12.
An danganta wannan mataki da bukatar daidaita ayyukan yakin neman zabe da nauyin gudanar da mulki.
Sai dai ADC ta ce Atiku zai kai kamfen dinsa dukkan jihohin kasar, inda za a ba shi damar ganawa da jama’a a wurare daban-daban.

Source: Facebook
Shettima ya soki Atiku
A wani labarin kuma, kun ji cewa mataimakin shugaban ƙasar Najeriya, Kashim Shettima, ya soki tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar.
Kashim Shettima ya tuna yadda Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya taimaka masa a siyasa tare da ba shi damar tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2007.
Asali: Legit.ng
