Mojtaba Khamenei: Halin da Lafiyar Jagoran Addinin Iran Ke Ciki

Mojtaba Khamenei: Halin da Lafiyar Jagoran Addinin Iran Ke Ciki

  • Shugaban majalisar dokokin Iran, Mohammad Bagher Ghalibaf ya bayar da tabbaci kan lafiyar jagoran kasar, Mojtaba Khamenei
  • Ghalibaf ya ce Khamenei ya nuna kuzari da kwarin gwiwa, tare da mai da hankali kan tattalin arziki, samar da muhimman kayayyaki da kare ƙarfin sayen jama’a
  • Wani babban jami’in Iran ya gargaɗi Amurka cewa duk wani sabon matakin da ta ɗauka zai fuskanci martani mafi tsanani da muni fiye da na baya​

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Birnin Tehran, Iran - Shugaban Majalisar Dokokin Iran kuma babban mai shiga tattaunawar diflomasiyya, Mohammad Bagher Ghalibaf, ya yi magana kan lafiyar Mojtaba Khamenei.

Mohammed Ghalibaf ya bayyana cewa Jagoran Addinin ƙasar, Mojtaba Khamenei, yana cikin ƙoshin lafiya.

An ji halin da Mojtaba Khamenei ke ciki
Shugaban majalisar dokokin Iran, Mohammed Bagher Ghalibaf Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Tashar Aljazeera ta ce kamfanin dillancin labarai na Tasnim, wanda ke da alaƙa da hukumomin Iran, ya ruwaito cewa Ghalibaf ya bayyana hakan ne bayan wani taro da ya yi da Khamenei a baya-bayan nan.

Kara karanta wannan

Shugaban hukumar Hisbah ya yi murabus daga mukaminsa, an ji dalili

Da yake jawabi ga ’yan majalisar dokokin ƙasar a wani zaman majalisa, Ghalibaf ya ce zai iya tabbatar musu da cewa jagoran yana cikin ƙoshin lafiya.

Ya ƙara da cewa Khamenei ya nuna kuzari, ƙwazo da kyakkyawan fata yayin ganawarsu, tare da nuna cikakkiyar fahimta game da manyan batutuwan ƙasa da ƙananan bayanai da suka shafe ta.

Me aka tattauna da Mojtaba Khamenei?

Ghalibaf ya bayyana cewa tattalin arziki na daga cikin muhimman batutuwan da suka tattauna da jagoran Iran.

A cewarsa, Khamenei yana bibiyar manyan alamu da ƙididdigan tattalin arzikin ƙasar, tare da gargaɗin cewa bai kamata a yi kuskuren tantance halin da tattalin arzikin yake ciki ba.

Ghalibaf ya ce Khamenei ya jaddada muhimmancin kauce wa ƙara gishiri ko rage muhimmancin bayanai yayin tantance yanayin tattalin arzikin ƙasar.

Haka kuma, jagoran ya ba da muhimmanci ga tabbatar da ci gaba da samar da kayayyakin da masana'antu ke buƙata, musamman albarkatun ƙasa da muhimman kayayyakin amfanin yau da kullum.

Kara karanta wannan

Gwamna Abba ya yi barazanar korar mukarraban gwamnatinsa, an ji dalili

Ya kuma jaddada buƙatar kare ƙarfin sayen jama'a da kuma tallafa wa rayuwar jami'an tsaron Iran da ke bakin aiki.

Iran ta gargaɗi Amurka kan daukar sabon mataki

A wani lamarin kuma, wakilin Jagoran Addinin Iran a rundunar juyin juya halin Musulunci ta IRGC, Abdollah Haji Sadeghi, ya gargaɗi Amurka kan duk wani sabon matakin da za ta ɗauka a kan Tehran.

A cewar Tasnim, Sadeghi ya ce Iran ta san raunin da abokan gabarta suke da shi, yana mai cewa duk wani sabon yunƙurin Amurka zai jawo martani mafi tsanani da muni fiye da wanda aka gani a baya.

Ya kuma bayyana cewa abokan gabar Iran sun yi kuskuren tunanin cewa kai hari kan shugabannin ƙasar da manyan kwamandojin sojojinta zai sa al'ummar Iran su juya wa gwamnatin ƙasar baya.

Mojtaba Khamenei na cikin koshin lafiya
Jagoran addini na kasar Iran, Mojtaba Khamenei Hoto: @IRNAnews
Source: Twitter

Netanyahu ya yi barazana ga Mojtaba

A wani labarin kuma, kun ji cewa firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya yi barazana ga Jagoran Addinin Iran, Mojtaba Khamenei.

Benjamin Netanyahu ya yi barazana ga Mojtaba Khamenei ni a wani bikin yaye jami’an sojojin Isra’ila.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng