Gwamna Ya Dauko Jaruman Fim Mata 2 da Suka Shahara, Ya ba Su Mukamai na Musamman

Gwamna Ya Dauko Jaruman Fim Mata 2 da Suka Shahara, Ya ba Su Mukamai na Musamman

  • Gwamnan jihar Enugu, Peter Mbah, ya nada fitacciyar jarumar Nollywood, Eucharia Anunobi, a matsayin babbar mataimakiyarsa ta musamman
  • Jarumar na cikin sababbin mataimaka 101 da gwamnan ya nada a mukamai daban-daban a jihar da ke Kudu maso Gabas
  • Jarumar mai shekaru 61 ta shiga cikin jerin fitattun jaruman Nollywood da aka ba mukaman siyasa a Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Enugu, Nigeria - Gwamnan jihar Enugu, Peter Mbah, ya nada fitacciyar jarumar Nollywood kuma mai shirya fina-finai, Eucharia Anunobi, a matsayin babbar mataimakiyarsa ta musamman.

Rahotanni sun nuna cewa jarumar za ta fike kujerar babbar mataimakiyar gwamna Peter Mbah ta musamman. kan wayar da kan mata a shiyyar Enugu ta Arewa.

Peter Mbah.
Gwamnan jihar Enugu, Peter Mbah a fadar gwamnatinsa Hoto: Peter Ndubuisi Mbah
Source: Twitter

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa an sanar da nadin Anunobi ne a cikin wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar Enugu, Chidiebere Onyia, ya fitar a watan Satumba.

Kara karanta wannan

Amurka ta kawo ɗauki mai zafi, manyan 'yan ta'adda sun fara guduwa a Najeriya

Gwamna Mbah ya nada jarumai mata 2

Jarumar na cikin sababbin hadimai 101 da aka nada a mukamai daban-daban a jihar Enugu, ciki har da masu ba da shawara na musamman da manyan mataimaka na musamman da kuma mataimaka na musamman.

Baya ga Anunobi, gwamnan ya kuma nada wata jarumar Nollywood, Rachael Okonkwo, a matsayin babbar mataimakiyarsa ta musamman kan bunkasa masana’antar fina-finai da kirkire-kirkire.

Sai dai Anunobi ce ta sanar da nadin nata a wani sako da ta wallafa a shafinta na Facebook a ranar Talata.

“Ya ku al’ummar kasata mai girma, Najeriya, da sauran duniya baki daya, ga sabuwar hadimar gwamna nan, yanzu abin ya zama hukumance.
“Ni ce babbar mataimakiya ta musamman kan wayar da kan mata a shiyyar Enugu ta Arewa ga gwamnan jihar Enugu, Peter Ndubuisi Mbah.”

Takaitaccen tarihin Eucharia Anunobi

An haifi Anunobi a Owerri, jihar Imo, kuma ta shahara a masana’antar Nollywood a shekarun 1990, inda ta fito a fina-finai sama da 90 kafin daga bisani ta zama mai wa’azin bishara.

Kara karanta wannan

Daga shan wani magani, an garzaya da ɗalibai fiye da 60 asibiti a jihar Katsina

Jarumar mai shekaru 61 ta shiga cikin jerin fitattun jaruman Nollywood da aka ba mukaman siyasa a Najeriya.

A watan Yulin 2011, an nada Nkiru Sylvanus, wata jarumar Nollywood, a matsayin mataimakiya ta musamman kan harkokin jihar Legas ga Rochas Okorocha, wanda a lokacin shi ne gwamnan jihar Imo.

A watan Afrilun 2022 kuma, gwamnan jihar Anambra, Charles Soludo, ya nada jarumin Nollywood, Bob-Manuel Udokwu, a matsayin mai ba shi shawara na musamman kan harkokin nishadi, yawon shakatawa da harkokin hutu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Tags: