Kasar waje
Yawan makaman nukiliya a duniya ya karu yayin da ake fargabar barkewar Yaƙin Duniya na III. Tahoto ya bayyana yadda kasashe ke ƙara adadin makaman nukiliyarsu.
Tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo ya bukaci 'yan Afrika su rabu da sunayen da suka samo asali daga mulkin mallaka da cinikin bayi da aka yi.
Gwamnatin Faransa ta jaddada aniyarta ta yaki da miyagun kwayoyi. Faransa za ta taimaka wa NDLEA wajen ba jami'anta horo da kwarewa a fannoni daban daban.
Fitacciyar mawakiya, Angie Stone ta rasu bayan hatsarin mota a Alabama. Ta shahara a hip-hop da R&B, ta kuma bar gagarumar gudunmawa ga duniyar waka.
Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa akwai bukatar manyan kasashen duniya su yi hakur, tare da yafe bashin da suke bin kasashen nahiyar.
Gwamnatin jihar Kano za ta dauki nauyin dalibai 1,002 don karatu a kasashen waje, domin bunkasa ilimi da bai wa matasa damar gogayya a matakin duniya.
An zabi shugaban sojojin saman Najeriya CAS Hassan Abubakar domin rike shugabancin sojojin saman Afrika. Za a gudanar da taron sojojin saman Afrika a Najeriya.
Rahotanni sun tabbatar da mutuwar dan kwallon Najeriya, Abubakar Lawal, wanda aka ce ya fado daga bene na uku a birnin Kampala da ke kasar Uganda.
Rahotanni sun ce Fadar Vatican ta tabbatar cewa Fafaroma Francis yana cikin mawuyacin hali bayan matsalar numfashi da kuma sauran matsaloli da ke damunsa.
Kasar waje
Samu kari