Jihar Borno
Rundunar yan sanda reshen jihar Borno, ta sanar da cewa, ta kama mutum 3 daga cikin waɗan da suka hito zanga-zangar nuna fushin su kan batanci a Maiduguri.
Jami'an tsaro da suka da sojoji, yan sanda, yan banga da sauran su, sun yi shawarar yadda zasu bullo wa lamari bayan an fara zargin wata ta ƙara batanci a Borno
Rundunar sojin haɗin guiwa MNJTF ta yi nasarar halaka manyan shugabannin kungiyar ISWAP da suka jagoranci kashe Abubakar Shekau na tsagin kungiyar Boko Haram.
Mummunan nufin yan ta'addan kungiyar Boko Haram/ISWAP ya koma kan mayaƙan su, inda wata nakiya da suka dasa ta tashi da yan uwan su mutum 6 sun sheƙa barzahu.
Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya sauke dukkan kwamishinoninsa daga mukamansu domin basu damar fitowa takara idan suna da ra'ayin hakan.
An samu wasu kungiyoyi masu zaman kansu da suka tarawa Babagana Umara Zulum kyautar N50m. Wadannan kungiyoyi su na jin dadin aikin da ya ke yi a jihar Borno.
Mohammed Ali Ndume, Sanata mai wakiltar mutanen kudancin Borno a majalisar dattawa, ya ce Arewa za ta fi amfana idan mulki ya koma kudu a shekara mai zuwa.
Kautukari da ke karamar hukumar Chibok ta jihar Borno a halin yanzu na fuskantar harI daga wasu da ake zargin mayakan kungiyar ISWAP da ke ta'addanci a yankin.
Dakarun jami'an tsaron hadin guiwa na kasashe (MNJTF) sun sheke 'yan Boko Haram 22 ko 'yan ta'addan ISWAP yayin da suke cin karensu ba babbaka a tafkin Chadi.
Jihar Borno
Samu kari