Mayakan kungiyar ISWAP sun kashe manoma 11 a jihar Borno

Mayakan kungiyar ISWAP sun kashe manoma 11 a jihar Borno

  • Yan ta'addan ISWAP sun kai hari kauyen Sabon-Gari da ke karamar hukumar Damboa ta jihar Borno
  • Maharan sun halaka manoma 11 ciki harda mace a farmakin wanda suka kai a ranar Asabar
  • Kauyen Sabon-Gari na a kimanin kilomita 125 daga garin Maiduguri, babbar birnin jihar Borno

Borno - Daily Trust ta rahoto cewa mayakan kungiyar ta’addanci ta ISWAP ta kashe akalla manoma 11 a yayin wani farmaki da ta kai yankin kudancin jihar Borno.

An tattaro cewa ISWAP ta kai mamaya kauyen Sabon-Gari da ke karamar hukumar Damboa ta jihar a ranar Asabar, 27 ga watan Fabrairu.

Mayakan kungiyar ISWAP sun kashe manoma 11 a jihar Borno
Mayakan kungiyar ISWAP sun kashe manoma 11 a jihar Borno Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

Kauyen Sabon-Gari na a kimanin kilomita 125 daga garin Maiduguri, babbar birnin jihar.

A cewar wata majiya ta tsaro, an gano kimanin gawarwaki bakwai a ranar Asabar sannan aka sake samun wasu hudu a ranar Lahadi.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Yan ta’addan sun yi garkuwa da malamin addini da wasu mutum 7 a jihar Neja

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Rahoton ya kuma kawo cewa wata majiya ta kuma bayyana cewar harda mace a cikin mutanen da aka halaka.

Majiyar ta ce:

“Mun gano gawarwakin manoma 11, duk an harbe du ne sau da dama, an binnesu daidai da koyarwar addinin Islama."

Mayakan ISWAP sun kashe mutane takwas, sun kona wani kauye a Borno

A gefe guda, mun kawo a baya cewa mayakan kungiyar ta’addanci ta ISWAP sun kashe akalla mutane takwas a wani hari da suka kai karamar hukumar Biu ta jihar Borno.

Jaridar The Cable ta rahoto cewa mayakan sun farmaki kauyukan Mandaragirau da Ghuma da ke karamar hukumar a daren ranar Asabar, 26 ga watan Fabrairu, inda suka kashe mazauna takwas da kuma jikkata wasu.

An tattaro cewa wasu majiyoyi na rundunar soji ta dakile wani hari da ISWAP suka kai hanyar Mandaragarau a safiyar Asabar.

Kara karanta wannan

Shugaban kasa a 2023: Wata kungiyar arewa ta goyi bayan Jonathan ya tsaya takara

Asali: Legit.ng

Online view pixel