Borno: Sojojin Najeriya Sun Kashe 'Yan ISWAP Da Dama, Sun Ƙwato Akuyoyi 5000

Borno: Sojojin Najeriya Sun Kashe 'Yan ISWAP Da Dama, Sun Ƙwato Akuyoyi 5000

  • Sojojin Najeriya na Operation Hadin Kai a Jihar Borno sun kwato akuyoyi guda 500 daga wasu da ake zargin 'yan ISWAP ne
  • Sojojin sun yi musayar wuta da 'yan ta'addan inda suka halaka kimanin guda biyar cikinsu kafin suka samu nasarar kwato dabobin
  • Wata majiya daga hukumar tsaro ta tabbatar da afkuwar lamarin inda ta ce masu akuyoyin sun aike da sakon neman dauki ne zuwa ga sojojin hakan yasa aka bi sahunsu

Borno - Dakarun sojoji karkashin Operation Hadin Kai a Jihar Borno sun kwato akuyoyi guda 500 daga mambobin kungiyar Islamic State West Africa Province (ISWAP) a karamar hukumar Jere, Jihar Borno.

Daily Trust ta rahoto cewa an kashe wasu da ake zargi yan ISWAP ne yayin gajeruwar musayar wuta tsakanin sojojin da barayin akuyoyin hakan ya yi sanadin mutuwar wasu daga cikin barayin.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Yan bindiga sun yi garkuwa da jami’in tsaro da wasu mutane a sabon harin Kaduna

Borno: Sojojin Najeriya Sun Kashe 'Yan ISWAP Da Dama, Sun Ƙwato Akuyoyi 5000
Sojojin Najeriya Sun Kashe 'Yan ISWAP a Borno, Sun Ƙwato Akuyoyi 5000. Hoto: Daily Trust
Asali: Twitter

Majiyar tsaro ta tabbatar da harin

Wata majiya, a cewar Daily Trust ta ce masu kiwon dabobin sun aike da sakon 'a zo a cece mu' zuwa ga kwamandan Operation Lafiya Dole, Manjo Janar Chris Musa, inda suka sanar da shi satar dabobin da aka musu.

"Sojojin sun bi sahun barayin dabobin suka tare su a wani wuri kusa da fitaccen gonar Cashew suka yi musayar wuta da su har sai da suka bindige biyar har lahira yayin da sauran suka tsere suka bar akuyoyin," a cewar majiyar ta tsaro.

Boko Haram sun dawo Chibok, sun kashe mutane, sun ƙona gidaje masu yawa

A wani labarin daban, kun ji cewa a kalla fararen hula uku ne suka riga mu gidan gaskiya a yayin da wasu da ake zargin yan Boko Haram ne suka kai hari a kauye da ke karamar hukumar Chibok a Jihar Borno da yammacin ranar Jumma'a.

Kara karanta wannan

Nasrun Minallah: Manyan kwamandojin Boko Haram 50, wasu mayaka 420 sun mika wuya ga sojoji a Borno

Kungiyar yan ta'addan sun afka kauyen Kautikari da ke kusa da gari Chibok misalin karfe 4 na yamma, suna harbe-harbe ba kakkautawa kuma suka kona gidaje da dama a cewar majiyoyi na tsaro, Daily Trust ta ruwaito.

A cewar majiyar, maharan sun iso ne a cikin motocci guda biyar dauke da bindiga mai harbo jiragen yaki kuma suka shigo cikin sauki ba tare da an nemi taka musu birki ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel