Yanzun Nan: Dakarun Sojoji sun halaka dan kunar bakin wake dauke da bama-bamai a Borno

Yanzun Nan: Dakarun Sojoji sun halaka dan kunar bakin wake dauke da bama-bamai a Borno

  • Yan ta'addan ISWAP da suka yi yunkurin kai harin kunar bakin wake sun fuskanci fushin dakarun sojin Najeriya
  • Rahoto ya nuna cewa yan ta'adda sun tura ɗayansu kai harin Bam kan soji, nan take sojojin suka bindige shi har lahira
  • Kungiyar ISWAP da ta balle daga Boko Haram na kara karfi bisa rahotanni, kuma ta kai wa sojoji hare-hare tun 2018

Borno - Yan ta'addan Boko Haram/ISWAP sun kaddamar da shirin kai farmaki nisan kilomita uku zuwa ƙauyen Ajigin Bulabulin, a jihar Borno.

Leadership ta tattaro cewa yan ta'addan sun yi nufin gano shirin dakarun rundunar soji na musamman dake sansani a yankin, domin mamayarsu.

Sai dai yan ta'addan sun gamu da tirjiya daga sojojin, nan take suka aika da ɗan kunan bakin wake, wanda sojojin suka halaka shi tun kafin ya isar da nufinsa.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Yan bindiga sun sake kai mummunan hari, sun halaka mutanen da ba'a san yawansu ba

Dakarun sojin Najeriya
Yanzun Nan: Dakarun Sojoji sun halaka dan kunar bakin wake dauke da bama-bamai a Borno Hoto: leadership.ng
Asali: UGC

Kungiyar ta'addancin ISWAP, wacce ta ɓalle daga Boko Haram na ƙara gina karfinta a yankin arewa maso gabashin Najeriya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wata majiya ta bayyana cewa ana tunanin ISWAP ta tara mayaƙa 3,500-5000, wanda hakan ya zarce wasu kungiyoyin yan ta'adda kamar JAS.

Tun daga shekarar 2018 zuwa yanzun, mayakan ISWAP sun kaddamar da hare-hare kan sansanonin sojojin Najeriya tare da kashe wasu da dama.

Wane mataki hukumomi ke ɗauka?

A kwanakin baya, gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umaru Zulum, ya yi gargaɗin cewa matukar aka yi sake da kungiyar ISWAP to zata fi Boko Haram hatsari.

Sai dai gwamnan ya bada shawarin cewa karfin soji kaɗai ba zai kawo karshen ayyukan ta'addanci ba, sai an haɗa da dabarun siyasa da yafiya.

Gwamnatin Najeriya ta ce zuwa yanzu, yan ta'adda sama da 30,000 tare da iyalansu ne suka mika wuya domin canza rayuwarsu a arewa maso gabas.

Kara karanta wannan

Hotuna: Shugaba Buhari ya dira birnin Nairobi, inda daga nan zai tafi Landan ganin Likita

A wani labarin na daban kuma Shugaba Buhari ya amince da makudan kudin kwaso yan Najeriya daga Ukraine

Karamin minista a ma'aikatar harkokin waje, Zubairu Dada, ne ya faɗi haka jim kaɗan bayan taron majalisar zartarwa a Abuja.

Ya ce jirage uku da zasu yi aikin zasu bar Najeriya zuwa kasashe huɗu dake makwaftaka da Ukraine.

Asali: Legit.ng

Online view pixel