Da Duminsa: Mayakan ISWAP sun mamaye sansanin sojojin Najeriya a jihar Borno

Da Duminsa: Mayakan ISWAP sun mamaye sansanin sojojin Najeriya a jihar Borno

  • Yan ta'addan ISWAP sun kai hari sansanin sojojin Najeriya dake Gamboru-Ngala, a jihar Borno domin ɗaukar fansa
  • Wani luguden wuta ta sama da sojojin suka kaddamar kan yan ta'addan ya halaka manyan kusoshin kwamandojin su
  • Lamarin ya fusata yan ISWAP, suka farmaki sansanin sojin kuma rahoto ya nuna cewa sun ƙona shi baki ɗaya

Borno - Kungiyar ta'addanci da ta balle daga kungiyar Boko Haram, ISWAP ta mamaye sasanin sojojin Najeriya dake Gamboru-Ngala a jihar Borno, ranar Lahadi da daddare.

Yan ta'addan sun farmaki sasanin sojin ne a makarantar Firamare dake garin Gamboru kuma suka tarwatsa dakarun soji, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

Haka nan yan ta'addan sun kone sansanin baki ɗaya a harin na ɗaukar fansa biyo bayan luguden wutan da sojoji suka musu a Tafkin Chadi.

Kara karanta wannan

An tsaurara tsaro: Majalisar jiha na shirin tsige mataimakin kakaki bisa kin jinin APC

Sojojin Najeriya
Da Duminsa: Mayakan ISWAP sun mamaye sansanin sojojin Najeriya a jihar Borno Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

Luguden wutan sojojin ya samu nasarar halaka manyan kwamandohin ISWAP da mayaƙan su a yankin Tafkin Chadi da kuma dajin Sambisa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Nasarar sojoji suka samu kan ISWAP

Ko a makon da ya gabata, ruwan wutan sojojin Najeriya ta sama ya halaka Amir Buba Danfulani da wasu manyan kwamandojin ISWAP aƙalla hudu a Tambuns da kuma Sambisa.

Danfulani na ɗaya daga cikin manyan kwamandojin da ISWAP ke ji da su, wanda ke jawo ra'ayin yan uwansa Fulani suna shiga kungiyar ta'addancin.

Kazalika shi ke kula da ayyukan yan ta'addan da suka haɗa da tura yan leken asiri da kuma masu karbo haraji a hannun mutane kamar yadda Sahara Reporter ta rahoto.

Rahotanni sun nuna cewa yan ta'addan sun fusata da nasarar sojoji a kansu, hakan ya sa suka nufi sansanin sojojin domin ɗaukar fansa.

Kara karanta wannan

Karin bayani: Sojin Najeriya sun ragargaji 'yan ISWAP da Boko Haram a Adamawa

Haka nan kuma an tattaro cewa sun dasa bama-bamai a garin Ngala a ƙarshen makon da ya gabata, wanda ya yi sanadin kashe farar hula ɗaya, wasu shida suka jikkata.

Ya Sojoji suka ji da lamarin?

Da aka tuntuɓe shi, kakakin rundunar sojojin ƙasan Najeriya, Onyema Nwachukwu, ya ce ba shi da masaniyar abin da ya faru, amma zai gudanar da bincike ya dawo ga wakilin mu.

A wani labarin kuma 'Bama-baman' da yan ta'adda suka ɗana ya fashe da dandanzon mutane a kauyen jihar Neja

Wani abun fashewa da ake tsammanin yan bindiga ne suka ɗana shi ya tashi a ƙauyen Galadima-Kogo, karamar hukumar Shiroro, jihar Neja.

Lamarin ya auku ne awanni kaɗan bayan yan bindiga sun kai hari kauyuka uku a jihar, wanda suke kusa da kauyen Galadima-Kogo.

Asali: Legit.ng

Online view pixel