Buhari ya tafi Nasarawa, Osinbajo ya dura birnin Maiduguri domin wata ziyara

Buhari ya tafi Nasarawa, Osinbajo ya dura birnin Maiduguri domin wata ziyara

  • Farfesa Yemi Osinbajo, mataimakin shugaban kasar Najeriya ya kai ziyara jihar Borno a yau Alhamis
  • Rahoton da muke samu daga majiyoyi sun bayyana cewa, Osinbajo ya samu tarbar gwamna Zulum na jihar ta Borno
  • Tafiyar Osinbajo ta yo daidai lokacin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tafi jihar Nasarawa wata ziyara

Maiduguri, jihar Borno - A yau Alhamis ne mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo ya dura birnin Maiduguri, jihar Borno a wata ziyarar rana daya da ya kai.

A cewar TVC, Osinbajo ya samu tarbar gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum yayin da ya sauka a jihar.

Ziyarar Osinbajo a jihar Borno
Buhari ya tafi Nasarawa, Osinbajo ya dura birnin Maiduguri a wata ziyarar aiki | Hoto: @tvcnewsng
Asali: UGC

Ziyarar Osinbajo dai na zuwa ne jim kadan bayan da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sauka a jihar Nasarawa a wata ziyarar aiki ta kwanaki biyu.

Kara karanta wannan

Yanzun Nan: Yan bindiga sun halaka babban jami'in Kwastam a garin Kaduna

Kalli hotunan ziyarar Osinbajo a Borno:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A wani bidiyon da jairdar Daily Trust ta yada a shafinta na Twitter, an ga mataimakin shugaban kasar a lokacin da yake kaddamar da ayyuka a jihar.

Kalli bidiyon:

Shugaba Buhari ya dira lafia, babban birnin jihar Nasarawa

A wani labarin, kunji cewa, shugaba Muhammadu Buhari ya isa garin Lafia, babban birnin Jihar Nasarawa domin ziyarar aiki na kwanaki biyu, rahoton Vanguard.

Shugaban kasar, wanda ya zo a cikin helicofta 5N-FG2, ya dira a filin tashi da saukan jirage na Lafia, misalin karfe 10 na safe.

Wadanda suka tarbe shi sun hada da gwamna mai masaukin baki, Abdullahi Sule, sai gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello, gwamnan Jihar Kebbi, Atiku Bagudu da mataimakin gwamnan Benue da wasu manyan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel