Bello Turji
Rundunar tsaron Najeriya ta sanar da kashe mataimakin Bello Turji mai suna Aminu Kanawa yayin farmaki. An kashe wasu tarin mayakan dan ta'addar a Sokoto da Zamfara.
Rundunar sojojin Najeriya na ci gaba da rike wuta a kan 'yan ta'adda, musamman mayakan Bello Turji da su ka addabi rayuwar mazauna Arewacin Najeriya.
Rahotanni sun tabbatar da cewa shugaban ƴan bindiga, Bello Turji ya saki dukkan waɗanda ya kama yayin da sojoji ke matsa masa lamba a jihar Zamfara.
Wasu rahotanni na zargin cewa shugaban 'yan bindiga, Bello Turji, yana cikin karamar hukumar Maradun a jihar Zamfara yayin da sojoji suka kara matsa masa.
Bello Turji ya kafa sabon sansani a dajin Dutsi, yana tsare da wadanda aka sace yayin da sojoji suka kara kaimi a Operation Fansan Yanma, domin murkushe yan ta'adda.
Tantirin shugaban 'yan bindiga da ya addabi mutanen yankin Arewa maso Yammacin Najeriya, Bello Turji, ya tara malaman tsubbu domin su yi masa addu'o'i.
Rundunar tsaron Najeriya ta ce Bello Turji cikakken matsoraci ne bayanya gudu ya bar mayakansa da dansa yayin farmaki da aka kai musu a yankin Zamfara.
Rahotanni sun tabbaar da cewa jagoran 'yan bindiga, Bello Turji ya koma sabon mafaka a gabashin Dutsin Birnin Yaro domin tserewa tsauraran farmakin sojoji a Fakai.
Hatsabibin shugaban 'yan bindiga, Bello Turji, ya umarci mayakansa da su yi wa dakarun sojoji kwanton bauna. Umarnin na Bello Turji na zuwa ne bayan an kashe dansa.
Bello Turji
Samu kari