Arewa
Matan Jato Aka sun bukaci gwamnati ta dakatar da kashe-kashe, ta kara tsaro, tare da kawo agajin gaggawa ga 'yan gudun hijira da rikici ya raba da gidajensu.
Ana zargin jami’an tsaron Sokoto da kwace shanu daga makiyaya tare da sayarwa, lamarin da ke haifar da tashin hankali. Jama’a sun bukaci ayi binciken gaggawa.
Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi ya kai ziyara domin yin ta'azziya ga gwamnan Filato, Caleb Mutfwang bayan rasuwar Sheikh Sa'id Hassan Jingir.
Rahotanni sun ce wasu da ake zargin yan bindiga ne sun kai farmaki gidan Alhaji Yusha’u Ma’aruf da ke kauyen Zakirai, karamar hukumar Gabasawa a Kano a yau Asabar.
Sheikh Ahmad Tijjani Yusuf Guruntum ya bayyana cewa duk wanda zai tsula tsiya a nan duniya, ya sani cewa babu makamawa akwai ranar da Allah zai masa hisabi.
Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya bayyana kudirin da yake da shi kafin ya bar mulki. Ya ce ya shirya barin jihar fiye da yadda ya same ta.
Tashar wutar lantarki ta kasa ta samu matsala, wanda ya haddasa duhu a wasu yankuna. Kamfanonin rarraba wuta na aiki don dawo da wutar cikin gaggawa.
Gwamnatin Najeriya ta sanya hannu kan kafa sabon kamfanin siminti a jihar Kebbi. Kamfanin zai samar da aiki ga mutane 45,000 idan aka kammala shi a jihar.
Imam Fuad Adeyemi ya soki matakin da wasu gwamnatocin jihohin Arewa suka dauka na kulle makarantu a lokacin watan Ramadan. Ya ce akwai siyasa a ciki.
Arewa
Samu kari