Arewa
A Imo, wasu ƴan bindiga da ake zargin ƴan IPOB ne sun kashe direbobi biyu sun kona tirela. An bukaci gwamnati ta shawo kan hare-haren da ake yi wa Hausawa.
‘Yan bindiga sun kai hari a Karongi, Baruten da ke Kwara, ina suka kashe mutum ɗaya, suka ƙone gidaje. An ce sojoji da 'yan sa kai sun fatattake su daga baya.
Hon. Aminu DanHamidu, shugaban karamar hukumar Bindawa a jihar Katsina, ya rasu bayan fama da rashin lafiya. Gwamnati da al’umma sun yi jimamin wannan rashi.
Yayin da ake bukukuwan sallah, Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero ya daga darajar mawaki Aminu Ladan Abubakar (Alan Waƙa) daga Ɗan Amanan Bichi zuwa Ɗan Amanan Kano
Rahotanni da muke samu sun tabbatar da cewa 'yan bindiga sun kuma kai wani mummunan farmaki a masallacin Dole Moriki da ke Zurmi a jihar Zamfara.
Rikicin sarauta ya sake barkewa a kauyen Muye da ke ƙaramar hukumar Lapai, ta jihar Niger bayan tsohon dagacin kauyen ya koma fada da karfi domin kwace kujerarsa.
Rahotanni sun tabbatar da cewa wani mutum mai shekaru 43 mai suna Kazeem daga unguwar Edun, Ilorin, ya mutu bayan ya fada rijiya bisa shan tabar ‘Colo’.
Rahotanni da muka samu sun ce rigima ta sake kunno kai a masarautar Zazzau bayan majalisar dokokin Kaduna ta karɓi ƙorafin cire Sarkin Zazzau, Ahmad Nuhu Bamalli.
Wani sanannen ɗattijon kasa daga Arewa, Alhaji Dabo Sambo ya bayyana cewa ba abin da ya fi ci wa ƴan Najeriya tuwo a kwarya kamar matsalar tsaro, ya gargaɗi Tinubu.
Arewa
Samu kari