Arewa
Fitaccen malamin addinin musulunci kuma kwamishinan harkokin addinai na jihar Sakkwato, Sheikh Dr. Jabir Sani Maihula ya yi rashi, mahaifinsa ya rasu a Sakkwato.
Sanata Abubakar Bello ya ba da N50m ga garin Mokwa da ambaliya ta shafa, yana mai in ta'aziyyar wadanda suka rasu da kuma roƙon Allah ya mayar da asarar da akayi.
Aƙalla mutum 43 aka kashe a hare-haren da 'yan bindiga suka kai Gwer da Apa a jihar Benue. Maharan sun kai farmaki da dare, inda suka buɗe wuta a garuruwan.
Dr. Lamido ya nemi Kudu maso Yamma su fitar da dukkan ‘yan takarar shugaban kasa a 2027, sannan a bai wa Kudu maso Gabas dama a 2031 don adalci da daidaito.
Tsohon ministan sadarwa, Farfesa Isa Pantami ya mika sakon jaje ga al'ummar Mokwa da ke jihar Neja bisa ambaliyar ruwan da ta afku a yankin da ke jihar Neja.
Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya bayyana cewa shugabanci abu ne mai natukar wahala kuma amana ce ta gudanar da dukiyar taakawa.
Rahotanni daga jihar Neja sun tabbatar da cewa tawagar masu aiki ceto sun tsamo gawarwakin mutane 115 zuwa ƙarfe 5 na yammacin jiya Juma'a a Mokwa.
Mutanen unguwar Nayinawa a jihar Gombe sun saye ragon layya wa gwamna Inuwa Yahaya. An yi wa shugaban gwamnonin Arewa kyautar ne saboda aikin kwari.
NiMet ta yi hasashen saukar mamakon ruwa a jihohi 14 daga 28 zuwa 30 ga Mayu, ta yi gargadin yiyuwar afkuwar ambaliya da iska mai karfi. An ce jihohi sun fara shiri.
Arewa
Samu kari