Arewa
Jami'an 'yan sanda sun cafke wasu mutane uku da ake zargin sun hallaka jami'in dan sanda a kauyen Konkiyel cikin karamar hukumar Darazo da ke jihar Bauchi.
Tsohon gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle ya zargi Gwamna Dauda Lawal kan rashin tabuka komai a kan harkar tsaro, ya ce ba ya neman shawarar magabatansa.
Wata kotu da ke zamanta a Abuja ta daure wata mata kan zargin cizon mai musu sulhu yayin da su ke fada, Alkalin kotun ya bukaci ta biya Naira dubu 500 na beli.
'Yan ta'adda sun hallaka wani shahararren malamin addinin Musulunci, Sheikh Ibrahim H. Musa da aka fi sani da Albanin Kuri a cikin gidansa da ke birnin Gombe.
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya rantsar da mace ta farko, Dije Audu Aboki a matsayin shugaban alkalan jihar, Abba ya nemi goyon bayanta a harkokin rusau
Wani kasurgumin dan daba da ake nema a Kano ruwa a jallo ya mika wuya ga hukumar 'yan sanda tare da neman afuwa da alkawarin cewa ba zai kara aikata laifi ba.
Shugabannin 'yan bindiga a Arewacin Najeriya sun bayyana cewa, yanzu kam sun gama aikin ta'addanci, za su ajiye makamai su rungumi zaman lafiya kowa ya huta.
Babbar kotun da ke zamanta a Ilorin da ke jihar Kwara ta yanke hukuncin kisa kan wani Mohammed Kazeem da zargin ya kashe makwabcinsa ana daf da daura aurensa.
Masu garkuwa sun afkawa fadar sarkin Gurku, Jibrin Mohammed a jihar Nasarawa tare da sace shi da mai dakinsa, jami'an 'yan sanda sun bazama cikin daji ceto su.
Arewa
Samu kari