Yan Bindiga Sun Sace Dan Sarkin Bungudu Da Kashe Wani Mutum 1 A Jihar Zamfara

Yan Bindiga Sun Sace Dan Sarkin Bungudu Da Kashe Wani Mutum 1 A Jihar Zamfara

  • ‘Yan bindiga sun sake kai farmaki a karamar hukumar Bungudu da ke jihar Zamfara tare da sace wasu mutane bakwai
  • ‘Yan bindigan sun kuma kashe wani mutum daya yayin kai farmakin bayan sun hargitsa hankulan mutanen garin da harbe-harbe
  • Wani mazaunin garin, Ishaq Bungudu ya koka kan yadda kullum ake kai hare-hare a Bungudu duk da kusancinsu da birnin Gusau

Jihar Zamfara - Wasu 'yan bindiga da safiyar yau Litinin sun sace wasu mutane bakwai da hallaka mutum daya a karamar hukumar Bungudu.

Wani mazaunin yankin, Ishaqa Bungudu ya bayyanawa Channels TV cewa 'yan ta'addan sun durfafi garin ne da muggan makamai.

'Yan bindiga sun sace dan sarki a Zamfara tare da hallaka wani mutum daya
Wasu Yan Bindiga Sun Kuma Kai Farmaki Jihar Zamfara Tare Da Sace Dan Sarkin Bungudu. Hoto: The Guardian.
Asali: UGC

Ya ce sun ta harbi sama don tsoratar da mutane kafin daga bisani suka yi ajalin mutum daya a yayin harbin.

Kara karanta wannan

Kwana Daya Bayan Rushewar Masallaci, Yan Bindiga Sun Halaka Mutum 2 a Zariya, Sun Sace Wani

Mutum nawa 'yan bindigan suka sace?

Ya ce ‘yan bindigan sun sace mutane bakwai da ya hada da dan sarkin Bungudu, Abdulrahman Hassan da wani ma’aikacin hukumar kula da harkar noma ta kasa da kasa (IFAD), Abubakar S/Fada.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ishaq Bungudu ya koka kan yadda hare-hare ke kara kamari a hedikwatar karamar hukumar duk da kusancin garin da birnin Gusau.

Ya bukaci gwamnan jihar, Dauda Lawal Dare da ya nada masu ba shi shawara a kan harkokin tsaro.

Wani shawara aka ba wa gwamnan a kan 'yan bindigan?

Ya ce:

“Kullum kawo mana hari ake, duk da kusancin da muke da shi da birnin Gusau, ba mu san meye ke faruwa ba.
“Gwamnati ba ta cewa komai, gwamnan ko masu ba shi shawara a kan harkikin tsaro ba shi da shi tun bayan rantsar da shi.

Kara karanta wannan

Yan Boko Haram Sun Halaka Mutum 5, Sun Yi Garkuwa Da Mata 7 a Jihar Borno

“Ya kamata ya nada masu ba shi shawara a kan harkokin tsaro saboda idan wani abu ya faru musan wa za mu kira don bayyana korafin mu.”

Kokarin jin ta bakin kakakin rundunar ‘yan sanda a jihar, ASP Yazid Abubakar bai yi nasara ba saboda rashin daukar wayar da aka kira shi, IReporteronline ta tattaro.

Sojin Sama Sun Hallaka Aliero Da Dankarami A Zamfara

A wani labarin, rundunar sojin sama ta yi ajalin wasu kasurguman shugabannin 'yan bindiga biyu a jihar Zamfara.

Wadanda aka kashen sun hada da Ado Aliero da Dankarami wadanda suka dade suna addabar mutanen jihar Zamfara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel