Zamfara: Matawalle Ya Soki Dauda Lawal Kan Rashin Nuna Kulawa A Tsaron Al’ummar Jihar

Zamfara: Matawalle Ya Soki Dauda Lawal Kan Rashin Nuna Kulawa A Tsaron Al’ummar Jihar

  • Tsohon gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle ya caccaki Gwamna Dauda Lawal kan rashin kulawa da tsaron al’umma
  • Matawalle ya bayyana haka ne yayin ganawa da Kungiyar ‘Yan Jaridu (NUJ) reshen jihar Zamfara a Abuja
  • Ya ce dole Dauda Lawal ya rinka neman shawara daga tsoffin gwamnoni don kawo karshen matsalar tsaro a jihar

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Zamfara – Tsohon Gwamna, Bello Matawalle na Zamfara ya ce ayyukan ‘yan bindiga da masu garkuwa kullum karuwa su ke a jihar musamman a birnin Gusau.

Gwamnan ya ce hakan bai rasa nasaba da rashin kulawa na Gwamna Dauda Lawal Dare a bangaren samar da tsaro ga al’umma.

Matawalle ya zargi Dauda Lawal da sake a harkar tsaro da ke damun jihar Zamfara
Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara, Bello Matawalle Ya Soki Gwamna Dauda Dare Kan Rashin Nuna Kulawa A Tsaron Al’umma. Hoto: TVC News.
Asali: Facebook

Matawalle ya bayyana haka ne yayin ganawa da Kungiyar ‘Yan Jaridu (NUJ) reshen jihar Zamfara a Abuja, TVC News ta tattaro.

Kara karanta wannan

Jarumin Gwamna Ya Jagoranci Jami’an Tsaro An Dura Gungun ‘Yan ta’adda Cikin Dare

Matawalle ya zargi Dauda Dare da rashin kulawa da al'umma

Tsohon gwamnan ya ce a yanzu jihar na fuskantar matsalar tsaro da ba a taba gani ba, inda ya gargadi Dare da ya bar korafe-korafe, ya mai da hankali wurin kawo zaman lafiya a jihar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce:

“Gwamna Dauda Lawal a yayin kamfe ya yi alkawarin kawo karshen matsalar tsaro a kankanin lokaci, amma bisa ga dukkan alamu ya gagara tabuka komai saboda rashin ba da kulawa.
“Mutane da dama ana kashe su da kuma garkuwa da su musamma a tsakiyar Gusau wacce ita ce babban birnin jihar.

Matawalle ya ce a lokacin mulkinsa, babu irin wannar matsalar, saboda ya ba da lokacinsa wurin tabbatar da kawo karshen tsaro, cewar Vanguard.

Ya yi Allah wadai da harin da aka kai a kananan hukumomin Maradun da Bunkure inda ya ce kawo karshen tsaro na bukatar neman shawara daga tsoffin gwamnonin jihar da sauran masu ruwa da tsaki, cewar People's Gazette.

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa Ya Amsa Kira, Ya Bai Wa Dan Ibo Babban Mukami a Gwamnatinsa

Matawalle ya ce lokacinsa ya na neman shawara a wurin magabata

Ya kara da cewa:

“Lokacin da na ke mulki, na nemi taimakon tsohon Gwamna Abdul’aziz Yari kan harkokin tsaro kuma hakan ya taimake ni.
“Idan Dauda Lawal ya damu da mutanen Zamfara wurin kawo karshen rashin tsaro, ya kamata ya nemi taimako daga sauran tsoffin gwamnoni da sauran masu ruwa da tsaki.”

Rundunar Sojoji Ta Murkushe Yan Bindiga 10 A Jihar Arewa, Ta Ceto Mutum 6

A wani labarin, rundunar soji a jihar Zamfara ta hallaka 'yan bindiga 10 tare da ceto wasu mutum shida.

Rundunar ta kai wannan harin ne a Gadan Zaima da Dan Marke da ke karamar hukumar Bukkuyum da ke jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel