Arewa
Wasu 'yan bindiga sun kai farmaki kauyukan jihar Neja inda suka halaka mutum daya tare da sace mutane fiye da 50 a kananan hukumomin Munya da Rafi da ke jihar.
An bayyana yawan ƙuri'un da kowace daga shiyyoyin Najeriya shida ta bai wa Shugaba Bola Tinubu lokacin zaɓe, da kuma yawan ministocin da kowace daga cikinsu.
Rundunar 'yan sanda a Kano ta ware makudan kudade har N300,000 ga duk wanda ya kawo bayanai da zai sa a kama wasu 'yan daba guda uku da ake nema ruwa a jallo.
Gwamna Abba Kabir ya bayyana cewa gwamnatinsa na bukatar Naira biliyan shida don samar da kujerun zama a makarantun firamare da sakandare don inganta ilimi.
Masu garkuwa sun hallaka wasu mutane biyu bayan sun kai musu kudin fansa a jihar Plateau, mutanen biyu sun gamu da ajalinsu yayin kokarin ceto 'yan uwansu.
Sanatan Adamawa ta Arewa, Ishaku Abbo ya bayyana yadda ya rubuta jarrabawar firamare a aji uku kuma ya yi nasara saboda shi na daban ne a cikin sauran dalibai.
Rundunar 'yan sanda a jihar Adamawa ta kwamushe mutane fiye da 100 kan zargin fasawa da kuma satar kayan gwamnati da sauran wurare na masu zaman kansu a jihar.
Wata mata mai koyon sana'a ta sace jariri dan kimanin watanni biyu na uwar dakinta a yayin bikin yaye dalibai a jihar Kwara a ranar Asabar 29 ga watan Yuli.
Malamin jami'ar Yobe a Arewacin Najeriya ya bayyana cewa, zai dauki mataki kan wani dalibinsa da ya masa maganar banza a kafar sada zumunta ta Facebook yau.
Arewa
Samu kari