Rundunar Soji Ta Hallaka 'Yan Bindiga 3 Tare Da Ceto Wasu 10 Daga Hannun Masu Garkuwa A Kaduna

Rundunar Soji Ta Hallaka 'Yan Bindiga 3 Tare Da Ceto Wasu 10 Daga Hannun Masu Garkuwa A Kaduna

  • Jami'an sojin Najeriya sun yi nasarar hallaka 'yan bindiga guda uku a wani samame a jihar Kaduna
  • Sojin sun kai farmakin ne a kauyukan kananan hukumomin Igabi da Chikun da ke jihar Kaduna
  • Rundunar ta tabbatar da ceto wasu mutane 10 da 'yan bindigan suka yi garkuwa da su bayan sun tsere sun barsu

Jihar Kaduna - Rundunar sojin Najeriya ta yi nasarar hallaka 'yan bindiga uku da kuma ceto wasu da aka yi garkuwa da su.

Rundunar yanki na daya da ke jihar ta kai samamen ne a kauyukan Kabode da Birnin Yero a kananan hukumomin Chikun da Igabi da ke jihar a jere.

Sojoji sun ceto mutane 10 daga masu garkuwa tare da hallaka 'yan bindiga uku
Wadanda Aka Ceto Daga Komar Masu Garkuwa Da Rundunar Sojin Najeriya Ta Yi. Hoto: Oasis Magazine.
Asali: Facebook

Yaushe aka kai harin kan 'yan bindigan?

Yayin zazzafan harin, rundunar ta yi ajalin gawurtattun 'yan bindiga uku tare da ceto wasu mutane 10 da aka yi garkuwa da su a kauyukan, PM News ta tattaro.

Kara karanta wannan

Rundunar Tsaro Ta Yi Kakkausar Suka Ga Masu Tunzura Ta Don Kifar Da Gwamnatin Tinubu, Ta Fadi Matsayarta

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

An kai samamen ne a jiya Juma'a 12 ga watan Agusta a kauyen Kabode da ke karamar hukumar Chikun bayan samun bayanan sirri daga wasu masu kishin kasa a yankin.

Rundunar ta yi artabu da 'yan ta'addan kafin suka yi nasarar hallaka su da kuma kwato bindiga kirar AK-47 dauke da alburusai 28.

Sauran kayan da aka samu a wurin 'yan bindigan akwai wayoyin salula uku da hular sojoji da layu da kuma kudi Naira 1,305, cewar Vanguard.

Meye 'yan bindiga suka tsere suka bari?

Har ila yau, rundunar ta shammaci wasu 'yan bindiga a kauyen Danbaba bayan samun bayanai na garkuwa da mutane a ranar 10 ga watan Agusta.

Rundunar ta kai samame a kauyen Birnin Yero a karamar hukumar Igabi inda 'yan bindigan suka tsere bayan hango jami'an tsaro tare da barin wadanda suka yi garkuwa da su mutum goma a wurin.

Kara karanta wannan

Rundunar Soji Ta Shammaci 'Yan Boko Haram Tare Da Aika 2 Daga Cikinsu Lahira, Ta Tarwatsa Su Daji

Tuni rundunar ta kwashi mutanen zuwa asibiti don duba lafiyarsu tare da hada su da iyalansu nan take.

Sojin Sama Sun Hallaka Aliero Da Dankarami A Zamfara

A wani labarin, rundunar sojin sama ta sheke gawurtattun shugabannin 'yan bindiga da suka hada da Ado Aliero da Dankarami a jihar Zamfara.

Aliero da Dankarami sun addabi yankuna da dama a jihar inda aka shafe shekaru ana artabu da su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.