Sojoji Sun Hallaka 'Yan Boko Haram 2 Tare Da Raunata Da Dama A Jihar Borno

Sojoji Sun Hallaka 'Yan Boko Haram 2 Tare Da Raunata Da Dama A Jihar Borno

  • Sojojin Najeriya na 'Operation Hadin Kai' sun hallaka 'yan Boko Haram guda biyu yayin wani samame a jihar Borno
  • Rundunar ta shammaci wasu 'yan ta'addan ne a kan yankin Kuka da ke karamar hukumar Konduga
  • Wannan na dauke ne a cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, Birgediya Janar Onyema Nwachukwu ya fitar a jiya Alhamis 10 ga watan Agusta

Jihar Borno - Rundunar sojin 'Operatiin Hadin Kai' ta shammaci wasu 'yan Boko Haram tare da hallaka su a karamar hukumar Konduga da ke jihar.

Kakakin rundunar, Birgediya Janar Onyema Nwachukwu shi ya bayyana a jiya Alhamis 10 ga watan Agusta.

Sojoji sun hallaka 'yan Boko Haram guda biyu a jihar Borno
Rundunar Sojoji Ta Yi Nasarar Hallaka 'Yan Boko Haram Tare Da Tarwatsa Sauran Daji. Hoto: Nigeria Army.
Asali: Twitter

Me Sojin suka ce kan hallaka Boko Haram?

Ya ce sojojin sun kai farmakin ne kan 'yan Boko Haram din a kan hanyar Kuka inda nan ne 'yan ta'addan ke yawan wucewa.

Kara karanta wannan

Gwamnan CBN Ya Fadi Abin Da Ya Jawo Naira Ta Sunkuya War-Was a Kasuwar Canji

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Nwachukwu ya ce jami'ansu sun fake ne tare da kai farmakin 'yar ba zata inda suka yi nasarar hallaka 'yan ta'addan biyu.

Hakan ya jawo tarwatsewar 'yan ta'addan ba tare da sun san inda suka nufa ba, Channels TV ta tattaro.

Bayan harin, rundunar ta samu alburusai da dama sai kuma abun fashewa da allura da kuma kudi Naira dubu 19 da dari hudu da sittin.

Yayin kokarin kakkabe 'yan Boko Haram a yankin, wani kasurgumin dan ta'adda ya mika wuya ga rundunar sojoji ta 222 da ke Geizuwa a karamar hukumar Konduga, TheCable ta tattaro.

'Yan Boko Haram nawa suka mika wuya?

Yayin mika wuyan, dan ta'addan ya gabatar da bindiga kirar AK-47 da alburusai da kuma sauran muggan makamai.

Rundunar na masa tambayoyin kwakwaf don sanin wani irin mataki ya kamata a dauka a gaba.

Kara karanta wannan

Nijar Ta Nada Shirgegen Mukami Yayin Da Kasar Ke Cikin Matsin Lamba Na Mika Mulki Daga ECOWAS, Bayanai Sun Fito

Shugaban hafsan sojin, Janar Taoreed Lagbaja ya yaba wa rundunar kan irin jajircewar da suke yi don ganin an kawo karshen ta'addanci a Najeriya baki daya.

Ya hore su da kada su gajiya wurin ci gaba da kakkabe 'yan ta'addan a yankunan.

Sojin Sama Sun Hallaka Aliero Da Dankarami

A wani labarin, rundunar sojin sama ta yi nasarar hallaka 'yan bindigan Arewacin Najeriya, Ado Aliero da Dankarami a wani samame a jihar Zamfara.

Aliero da Dankarami sun addabi mutanen yankin inda aka dade ana artabu da su kafin samun wannan nasara a kansu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel