Rashin Tsaro: Hukumar DWI Ta Bukaci Tinubu Ya Sanya Dokar Ta Baci A Jihar Zamfara

Rashin Tsaro: Hukumar DWI Ta Bukaci Tinubu Ya Sanya Dokar Ta Baci A Jihar Zamfara

  • An bukaci Gwamnatin Tarayya da ta saka dokar ta baci a jihar Zamfara saboda rashin tsaro da ya yi katutu
  • Hukumar DWI mai rajin tabbatar da dimokradiyya ta ce dokar ta baci ce kawai za ta tabbatar da natsuwa a wurin mutanen jihar
  • Hukumar ta soki Gwamna Dauda Lawal Dare da irin yadda ya ke gudanar da matsalar tsaro a jihar ba tare da nuna kulawa ba

FCT, Abuja - Hukumar Dabbaka Dimokradiyya (DWI) ta bukaci gwamnatin Tarayya ta saka dokar ta baci a jihar Zamfara.

Hukumar ta bayyana haka ne ganin yadda rashin tsaron da ya yi katutu a yankunan jihar tare da rasa rayuka.

DWI ta bukaci Gwamnatin Tarayya ta saka dokar ta baci a jihar Zamfara
Hukumar DWI Ta Kirayi Gwamnatin Tarayya Ta Sanya Dokar Ta Baci A Zamfara. Hoto: PLUS TV Africa.
Asali: Youtube

Me DWI ta ce gane da rashin tsaro?

Kakakin hukumar, Sanusi Ali Mohammed shi ya bayyana haka a cikin wata sanarwa a ranar Litinin 14 ga watan Agusta a Abuja, cewar Vanguard.

Kara karanta wannan

An Kuma: 'Yan Bindiga Sun Sace Wasu 7 Da Dan Mashahurin Sarki A Jihar Arewa, Sun Yi Ajalin Mutum 1

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya ce wannan kira ya zama dole ganin yadda rashin tsaro ke kara tabarbarewa musamman cikin watanni biyu ta suka wuce.

Ya kara da cewa duk da kokarin gwamnatin da ta shude wurin dakile rashin tsaron, abin kullum karuwa ya ke musamman birnin Gusau da ke daf da fadawa hannun 'yan bindigan, Newstral ta ruwaito.

Ya ce:

"Mun fahimci cewa tun a watan Yuni, rashin tsaro kullum karuwa ya ke inda ake kashe mutane babu kakkautawa da kuma sace mutane tare da karbar kudin fansa.
"Masu garkuwa na cin karensu babu babbaka yayin da suka wargaza yankuna da dama a jihar.
"Hatta majalisar jihar ta koka da cewa yadda 'yan bindigan ke aika-aika kamar babu gwamnati a jihar.

Wace hanya za a bi don dakile rashin tsaron?

DWI ta soki gwamnatin Dauda Lawal ganin yadda ya ke riko da harkar tsaro a jihar da rashin nuna kulawa, PLUS TV Africa ta tattaro.

Kara karanta wannan

Tsohon Abokin Tafiyar Buhari Ya Ambato Kuskuren Da Shugaba Tinubu Ya Fara Daga Hawa Mulki

Ta ce:

"Muna kira da a yi gaggawar saka dokar ta baci a jihar saboda an zubar da hawaye da kuma jini iyaka a cikin watanni biyu ganin yadda gwamnatin jihar ta yi biris da harkar tsaro.
"Muna jan hankalin Gwamnatin Tarayya cewa dokar ta baci ce kadai za ta tabbatar wa mutanen jihar samun natsuwa."

'Yan Bindiga Sun Sace Dan Sarki Da Wasu 7 A Zamfara

A wani labarin, wasu 'yan bindiga sun kai farmaki karamar hukumar Bungudu tare da sace wasu mutane bakwai ciki har da dan sarkin garin.

'Yan bindigan har ila yau, sun kashe mutum daya yayin kai farmakin a safiyar yau Litinin 14 ga watan Agusta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel