Tsageru Sun Sace Sarki Ajin Farko Tare Da Matarsa A Arewacin Najeriya, An Bazama Nemansu

Tsageru Sun Sace Sarki Ajin Farko Tare Da Matarsa A Arewacin Najeriya, An Bazama Nemansu

  • Masu garkuwa sun sace wani sarki ajin farko a jihar Nassarawa tare da matarsa a fadarsa da ke garin Gurku
  • Sarkin mai suna Jibrin Mohammed an sace shi ne tare da matarsa a ranar Lahadi 6 ga watan Agusta da dare
  • Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, DSP Rahman Nansel ya tabbatar da sace sarkin inda ya ce sun tura jami'ansu don ceto wadanda aka sacen

Jihar Nasarawa - Masu garkuwa sun sace sarkin Gurku, Jibrin Mohammed a fadarsa tare da matarsa a jihar Nasarawa.

An sace babban sarkin ne a jiya Lahadi 6 ga watan Agusta da dare a fadarsa da ke garin tare da mai dakinsa a karamar hukumar Karu da ke jihar.

Masu garkuwa sun sace sarki da mai dakinsa a jihar Nasarawa
Masu Garkuwa Sun Addabi Jihar Nasarawa Musamman Yankunan Karkara. Hoto: Leadership.
Asali: UGC

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, DSP Rahman Nansel shi ya bayyana haka ga gidan talabijin na Channels a yau Litinin 7 ga watan Agusta.

Kara karanta wannan

Ku Yi Hakuri: Shugabannin 'Yan Bindiga a Arewa Sun Nemi Afuwa, Za Su Ajiye Makamai

Kakakin rundunar a jihar ya bayyana kara tura jam'ian tsaro yankin

Ya ce sun samu labarin sace sarkin ne a fadarsa da ke yankin Mararraba a cikin karamar hukumar Karu da ke jihar.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Rahman ya ce sun tura jami'an tsaro da 'yan kungiyar sa kai a cikin dazukan yankin don ceto sarkin da iyalinsa, Politics Nigeria ta tattaro.

Har ila yau, ya tabbatar da cewa ba a samu nasarar ceto wadanda aka sacen ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto.

'Yan sanda sun bazama dazuka neman masu garkuwan

A kokarin ceto sarkin da iyalinsa, an kara tura jami'an 'yan sanda da kuma bangaren kwararru na hana garkuwa zuwa dazukan don kwato wadanda aka sacen, cewar Punch.

Jihar Nasarawa na fama da hare-haren 'yan bindiga musamman a yankunan karkara da ke jihar.

Kara karanta wannan

Kitimurmura: Soja mace ta fusata, ta harbe na gaba da ita a wurin aiki a jihar Arewa

A kwanan nan 'yan bindiga sun kai hari gidan tsohon minista Labaran Maku a lokacin mulkin Goodluck Jonathan tare da raunata mutunre da dama.

Masu Garkuwa Sun Farmaki Gidan Tsohon Minista A Jihar Nasarawa, Sun Raunata Masu Gadi Mutum 3

A wani labarin, 'yan bindiga da ake kyautata zaton masu garkuwa ne sun kai farmaki gidan tsohon minista, Labaran Maku tare da raunata masu gadinshi mutum uku.

'Yan bindigan sun kai harin ne da misalin karfe 7:50 na dare a gidansa da ke Ola a karamar hukumar Akwanga a cikin jihar Nasarawa.

Daya daga cikin masu gadin ya bayyana cewa maharan sun haura ta katanga bayan sun yi ta dukan kofar gidan bai budu ba kuma sun fahimci babu wanda zai bude musu kofar gidan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel