Bola Tinubu
Dukkan jakadun Najeriya za su dawo gida nan da karshen watan Oktoba biyo bayan umarnin shugaban kasa Tinubu cewa su gaggauta dawowa bayan dakatar dasu aiki.
An bayyana bude iyakokin kasar Gabon bayan shafe kwanaki da rufe ta bayan yin juyin mulkin soja a makon da ya gabata. An abyyana dalilin yin juyin mulkin kasar.
Shugaban Bola Ahmed Tinubu ya amince da shirin rabon gilashin ido fiye da miliyan 5 ga yan Najeriya masu fama da lalurar gani a sassan kasar don tallafa musu.
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya yi wa jakadan ƙasar a Burtaniya kiranye, ya umarci ya tafi hutun watanni biyu kuma ya gode masa bisa aikin da ya yi.
Kamfanin BUA karkashin jagorancin biloniya, Abdussamad Rabiu ya shirya rage farashin siminti a fadin Najeriya baki daya don bunkasa tattalin arzikin Najeriya.
Mai girma ministan labarai, Mohammed Idris, ya kore duk fargabar cewa sojoji za su kwace mulki a Najeriya. Idris ya ce kasar ta dade da wuce wannan matakin.
A lokacin da gwamnatin tarayya ta kafa NASENI, watakila Khalil Suleiman Halilu bai wuce shekara daya a Duniya ba, a yau shi aka nada ya jagoranci wannan hukuma.
Tsohon shugaban bankin UBA kuma shugaban kamfanin Heirs Holdings, Tony Elumelu ya bayyana cewa ko kaɗan shugaba Tinubu bai fara tunanin naɗa shi gwamnan CBN ba.
Ministan kudi, Wale Edun ya shaida cewa za su yi kokari wajen toshe kafofin facaka a gwamnati domin a iya kashe dukiyar al’umma ta hanyoyin da su ka fi dacewa.
Bola Tinubu
Samu kari