Majalisa Ta Bukaci Tinubu Ya Dakatar da Turo Kudaden Kananan Hukumomi Kan Dalili 1 Tak, Ta Fusata

Majalisa Ta Bukaci Tinubu Ya Dakatar da Turo Kudaden Kananan Hukumomi Kan Dalili 1 Tak, Ta Fusata

  • Majalisar Dattawa ta shawarci Shugaba Tinubu da ya dakile kudaden kananan hukumomi
  • Majalisar ta bayyana haka ne a yau ta bakin Sanata Abba Moro inda ya ce akwai jihohin da ba su da shugabanni
  • A bangarenshi, Adams Oshiomole ya ce akalla akwai jihohi 16 a yanzu da ba su da zababbun shugabanni

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja – Majalisar Dattawa ta bukaci Shugaba Tinubu da ya dakatar da turo kudaden kananan hukumomin da babu shugabanni.

Wannan na zuwa ne yayin gabatar da kuduri da Sanata Abba Moro mai wakiltar Benue ta Kudu ya yi.

Majalisa ta shawarci kan tura kudaden kananan hukumomi a jihohi
Majalisa ta shawarci Tinubu ya dakatar da tura kudaden kananan hukumomi. Hoto: Godswill Akpabio.
Asali: Facebook

Mene Majlisar ta bukaci Tinubu?

Moro ya gabatar da kudurin ne a yau Alhamis 1 a watan Disamba yayin zaman Majalisar a Abuja, cewar Leadership.

Kara karanta wannan

"Cin zabe sai an hada da rauhanai" Shehu Sani ya yi wa Doguwa martani

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanatan ya ce ya kamata a dauki matakin gaggawa kan rusa shugabannin kananan hukumomi da aka yi a jihar Benue.

Majalisar ta yi Allah wadai da rusa zababbun shugabannin a tsarin dimukradiyya a jihar Benue da ma sauran jihohi da abin ya faru.

Har ila yau, Majalisar ta umarci Gwamna Alia da ya yi amfani da rantsuwar da ya dauka wurin yin biyayya ga kundin tsarin mulki.

Wane martani sauran sanatocin su ka yi?

Moro ya ce akwai hukuncin kotu kan gwamnan da ‘yan Majalisun jihar da ma sauran da kusa da shi kan taba martabar shugabannin kananan hukumomin.

Ya kara da cewa da gwamnan da kuma Majalisar babu wanda ya daukaka kara kan wannan doka da kotu ta yi, cewar PM News.

A martaninshi, Sanata Adams Oshiomole ya ce a yanzu jihohin Najeriya 16 ne ba su da zababbun shugabannin kananan hukumomi a jihohinsu.

Kara karanta wannan

Yadda cikin shekara 24 Najeriya ta yi abin da Amurka ta kasa yi sai bayan shekara 185, Akpabio ya bayyana

Ya ce Majalisa ya kamata ta umarci ma’aikatar kudade da su dakatar da ba su kudade saboda wannan matsalar.

Sanata Ali Ndume ya goyi bayan wannan kuduri tare da wasu sanatoci kamar Abdulfatai Buhari daga Oyo ta Arewa.

Mun kafa tarihi a shekaru 24 kacal, Akpabio

A wani labarin, shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ya bayyana cewa Najeriya ta kafa tarihi a cikin shekaru 24

Ya ce wannan abin kirki da kasar ta cimma ya dauki Amurka shekaru 185 kafin su ka cimma shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel