Kasafin Kudi: Rage Talauci da Abubuwa 8 da Bola Tinubu Zai Ba Muhimmanci a 2024

Kasafin Kudi: Rage Talauci da Abubuwa 8 da Bola Tinubu Zai Ba Muhimmanci a 2024

  • Akwai wuraren da gwamnatin tarayya ta zaba, ta fi ba su fifiko a wajen shirya kasafin kudin shekara mai zuwa
  • Bola Ahmed Tinubu ya fahimci halin da ake ciki, ya bada karfi wajen rage wadanda ke rayuwa a kuncin talauci
  • Tinubu ya sha alwashin gyara tattalin arzikin da ke fuskantar tsadar kaya, karancin kudin shiga da rashin aikin yi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abuja - A kasafin kudin shekara mai zuwa ta 2024, Bola Ahmed Tinubu ya ce babban abin da zai dage a kai shi ne tsaro da zaman lafiya.

Fadar shugaban kasa ta ce Mai girma Bola Ahmed Tinubu ya sha alwashin samar da ayyukan yi tare da farfado da tattalin arzikin Najeriya.

TINUBU
Muhimman abubuwa a kasafin kudi 2024 Hoto: @Dolusegun16
Asali: Twitter

Tinubu zai gyara tsaro da tattalin arziki

A jawabin da ya gabatar, Bola Tinubu ya ce za ayi wa tsarin tsaro kwaskwarima a Najeriya domin a tsare rayuka da dukiyoyin jama’a.

Kara karanta wannan

Ministoci 9 sun tashi da kaso mafi tsoka a kasafin kudin naira tiriliyan 27 da Tinubu ya gabatar

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kundin kasafin kudin shekarar 2024 ya fi karkata zuwa ga wasu abubuwa takwas kamar yadda Ajuri Ngelale ya sanar a wani jawabi jiya.

Daga cikinsu akwai samar da hanyar da masu hannun jari za su kawo kudi domin yin kasuwanci wanda hakan zai inganta tattalin arziki.

Kasafin kudi: Harkar ilmi da bada tallafi

Gwamnatin Tinubu za ta kara tsayawa tsayin-daka wajen yakar talauci da zarar an amince da kasafin kudin na 2024 a majalisun tarayya.

Kasafin kudin 2024 ya bada karfi sosai a abin da ya shafi cigaban al’umma, musamman kananan yara wanda sai da su ake cigaba.

Za a kawo tsare-tsare da za su taimaka kasuwanci domin tattalin arzikin kasar ya motsa da 3.76% har a rage hauhawar farashi zuwa 21.4%.

Jerin abubuwan da kasafin 2024 zai fi ba karfi

1. Tsaron kasa da zaman lafiyar al’umma

Kara karanta wannan

Akpabio ya bukaci Tinubu ya haramtawa ministocinsa fita kasashen waje, ya bayyana dalili

2. Samar da ayyukan yi ga jama’a

3. Farfado da tattalin arziki

4. Shimfida wurin zuba hannun jari

5. Inganta haraji da kudin shiga

6. Tsare-tsaren cigaban al’umma

7. Rage talauci

8. Bunkasa rayuwar mutane

Tsaro da ilmi sun samu N6tr a kasafin 2024

A kasafin kudin na 2024, ana da labari Badaru Abubakar, Tahir Mamman, Adebayo Adelabu, Festus Keyamo za su kashe Tiriliyoyi a 2024.

Bola Tinubu ya kara adadin kudin da aka saba kashewa a shekara a harkar ilmi da tsaro. Kasafin lafiya da tsaro sun karu da 23.15% da 46.39%.

Asali: Legit.ng

Online view pixel