Shugaba Tinubu Ya Buƙaci Mataimakin Gwamnan APC Ya Sa Hannu Kan Takardar murabus kan abu 1 tal

Shugaba Tinubu Ya Buƙaci Mataimakin Gwamnan APC Ya Sa Hannu Kan Takardar murabus kan abu 1 tal

  • Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya nemi mataimakin gwamnan Ondo ya sa hannu kan takardar murabus kuma ya kai masa
  • Wannan na ɗaya daga cikin matakan da aka aminta da su a wurin taron sulhunta rikicin siyasar jihar Ondo
  • Kwamishinar yaɗa labarai ta jihar, Bamidele Ademola-Olateju, ita ce ta bayyana haka a wata hira ranar Jumu'a

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Ondo - Kwamishinar yaɗa labarai ta jihar Ondo, Bamidele Ademola-Olateju, ta bayyana abubuwan da aka cimma matsaya a zaman sulhunta rikicin siyasar jihar Ondo.

Ta ce Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya umarci mataimakin gwamnan Ondo, Lucky Aiyedatiwa, ya sa hannu kan takardar murabus mara kwanan wata ya kai masa.

Kara karanta wannan

Wasu hadimai sun yi jabun sa hannun gwamnan APC don sace kuɗi? Gaskiya ta bayyana

Yadda Tinubu ya sasanta rikicin jihar Ondo.
Ondo: Shugaba Tinubu Ya Bukaci Mataimakin Gwamna Ya Sa Hannu a Takardar Murabus Hoto: channelstv
Asali: UGC

Ademola-Olateju ta faɗi haka ne a wata hira da gidan talabijin na Channels cikin shirin 'Lunchtime Politics' wanda aka watsa ranar Jumu'a, 1 ga watan Disamba, 2023.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Idan baku manta ba a ranar Alhamis, Aiyedatiwa, ya jagorsnci taron majalisar zartarwa bayan tsawon lokacin yana takun saƙa da Gwamna Rotimi Akeredolu.

Taron majalisar zartaswar dai ya biyo bayan kiran da Tinubu ya yi wa bangarorin da ke adawa da juna, tsagin Akeredolu da tsagin Aiyedatiwa domin warware rikicin siyasar jihar.

Shiga tsakanin da Tinubu ya yi na nufin Akeredolu zai ci gaba da zama gwamnan jihar Ondo yayin da Aiyedatiwa zai riƙe matsayinsa na mataimakin gwamna, in ji fadar shugaban kasa.

Tinubu ya nemi Aiyedatiwa ya sa hannu kan takardar murabus

Da take jawabi a cikin hirar, kwamishinar yaɗa labarai ta ce Shugaban Ƙasa ya umarci mataimakin gwamnan ya sa hannun kan takardar murabus wacce ba kwanan wata.

Kara karanta wannan

Mataimakin gwamnan APC zai rubuta takardar murabus daga muƙaminsa, sahihan bayanai sun fito

A cewarta, Tinubu ya yi haka ne domin kaucewa abinda ka iya tasowa daga ɓangaren mataimakin gwamnan nan gaba, cewar rahoton Daily Post.

A wani ɓangaren jawabin da ta yi, Ademola-Olateju ta ce:

“Ya nemi takardar murabus din Honorabul Lucky Aiyedatiwa, mataimakin gwamna wadda babu kwanan wata a jiki saboda ko wani abu zai faru nan gaba."

Gwamnatin Jigawa zata ɗauki ma'aikata

A wani rahoton na daban Gwamnatin Jigawa karkashin Gwamna Umar Namadi za ta ɗauki ma'aikatan lafiya 1,124 domin inganta harkokin lafiya.

Kwamishinan yaɗa labarai na jihar, Alhaji Sagir Musa, ya ce majalisar zartarwa ta amince da haka a zaman ranar Alhamis.

Asali: Legit.ng

Online view pixel