Zaben 2027: An Bayyana Hanya 1 da PDP Za Ta Bi Domin Kawar da Jam'iyyar APC a Mulki

Zaben 2027: An Bayyana Hanya 1 da PDP Za Ta Bi Domin Kawar da Jam'iyyar APC a Mulki

  • Ɗaya daga cikin manyan jam'iyyun siyasar Afirka, PDP, ta mulki Najeriya na tsawon shekaru 16, daga 1999 zuwa 2015
  • Wacce ake yi wa kallon babbar jam’iyyar adawa a ƙasar nan, PDP na fafutukar ganin ta kawar da jam’iyyar All Progressives Congress (APC)
  • Wani masani kan harkokin siyasa, Segun Akinleye, ya bayyana fargabar cewa idan ba a yi amfani da dabarar da ta dace ba, Najeriya na iya zama ƙasa mai jam’iyya ɗaya

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Wani mai sharhi kan al'amuran siyasa, Akinleye Oluwasegun, ya ce "hanya mafi kyau" babbar jam'iyyar adawa ta Najeriya, PDP, za ta iya kayar da jam'iyyar APC mai mulki a zaɓen shugaban ƙasa na 2027 "shi ne ta hanyar haɗaka".

Kara karanta wannan

PDP ta shiga tangal-tangal yayin da sabuwar rigima ta kunno kai kan rikicin Wike da Fubara

Akinleye ya yi nuni da cewa, Atiku Abubakar, ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar PDP a zaɓen 2019 da 2023, ya riga ya yi kira da a yi amfani da haɗaka.

Akinyele ya shawarci jam'iyyar PDP
Hankali ya fara koma wa kan zaben 2027 Hoto: Akinleye Oluwasegun, Atiku Abubakar
Asali: Facebook

"Kawar da APC zai yi wahala,” Akinleye

Manazarcin, ya nuna damuwarsa kan cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, wanda ɗan siyasa ne mai fada a ji a Najeriya, "ba zai bari a samu haɗin kan ƴan adawa ba".

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Akinleye ya ba da misali da rikicin da ke tsakanin jam'iyyar Labour Party (LP), wanda ya ce wasu daga waje ne ke rura wutarsa.

Ya shaida wa Legit.ng a wata tattaunawa cewa:

"Hanya mafi inganci da za a iya kayar da APC ita ce haɗaka, kuma Atiku ya riga ya yi kira da hakan, amma akwai matsala."
"Mu yi la’akari da tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, Buhari ya tsaya takara a jam’iyyar All Nigeria Peoples Party (ANPP) a 2003 da 2007, a shekarar 2017 ya tsaya takara a ƙarƙashin rusasshiyar jam’iyyar Congress for Progressive Change (CPC), amma a 2014, an samu haɗewar da Tinubu ya jagoranta, kuma a shekarar 2015, an kori PDP daga ofis."

Kara karanta wannan

Zaben Edo: Wike ke daukar nauyin takarar da gwamnan da Philip Shaibu ya fito? Jigon PDP ya fadi gaskiya

"Wannan ita ce hanya mafi sauƙi don kayar da jam’iyya mai mulki. Hakan ya faru a Laberiya kwanan nan lokacin da George Weah ya sha kaye kafin zaɓaɓɓen shugaban ƙasar ya samu damar haɗa ƴan adawa wuri guda."

Wane ƙalubale PDP za ta fuskanta?

Manazarcin ya cigaba da cewa:

"Yanzu, 'matsalar' ita ce ƴan adawa sun rasa damar su a zaɓen shugaban ƙasa na Fabrairu. Tinubu, a matsayinsa na haziƙin ɗan siyasa, ba zai ba da damar haɗa kan ƴan adawa ba."
"Mu dubi jam’iyyar PDP da rikicin cikin gida, ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, yana da ƙafa ɗaya a PDP, ɗaya kuma a APC, Seyi Makinde na cikin gwamnonin da suka yi taurin kai a 2023, har yanzu yana jam’iyyar PDP. Bala Mohammed shugaban ƙungiyar gwamnonin PDP yana magana kamar ɗan jam'iyyar APC."

An Fara Shirin Gyara a PDP

A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta fara shirye-shiryen yadda za ta yi gyara domin tunkarar jam'iyyar APC mai mulki

Jam'iyyar za ta kira wani ɗan ƙaramin gangami domin cike gurabun da ake da su a kwamitin NWC, wanda hakan zai taimaka mata wajen tunkarar zaɓe mai zuwa na 2027.

Asali: Legit.ng

Online view pixel