Bola Tinubu
Majalisar dattijai ta tabbatar da nadin Adama Oluwole Oladapo a matsayin babban darakta na hukumar kula da ayyukan samar da iskar gas ta Najeriya (NMDGIFB).
A karshe, Gwamnatin Tarayya ta janye tuhumar da ta ke yi wa dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar AAC, Omoyole Sowore kan zargin cin amanar kasa.
Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewa nan ba da jimawa ba za a magance matsalolin da suka taru suka dabaibaye kasar nan.
Gwamnatin shugaban kasa Bola Tinubu za ta raba kayan hatsi kyauta ga talakawan Najeriya, Abubakar Kyari, ministan noma da tsaron abinci ya bayyana.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu zai gana da daukacin gwamnonin Najeriya 36 a fadarsa da ke Abuja kan halin da kasa ta ke ciki kafin ya shilla zuwa Habasha.
Sarkin Musulmi da sauran Sarakunan Arewa sun yi zama a Kaduna, sun fadawa kan su gaskiya. Sarakunan sun ce lamarin wahalar rayuwa da yunwa ta kai intaha.
Ministan wutar lantarki, Adebayo Adelabu, ya bayyana cewa gwamnatin tarayyar Najeriya ba za ta iya ci gaba da bayar da tallafin wutar lantarki ba.
Babbar jam'iyyar adawa ta ƙasa PDP ta tabbatar da tsohon shugaban majalisar dattawa, Sanata Wabara a matsayin shugaban kwamitin amintattu BoT na ƙasa.
Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Sa’ad Abubakar ya nuna damuwa kan yadda aka bar matasa babu aikin yi inda ya ce hakan babban barazana ce ga Najeriya.
Bola Tinubu
Samu kari