Tsadar Rayuwa: Ganduje Ya Fadi Lokacin da Sauki Zai Zo Kan Halin da Ake Ciki a Kasa

Tsadar Rayuwa: Ganduje Ya Fadi Lokacin da Sauki Zai Zo Kan Halin da Ake Ciki a Kasa

  • Shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya yi magana kan halin ƙuncin da ake ciki a ƙasar nan
  • Ganduje ya bayyana cewa nan ba da jimawa ba abubuwa za su daidaita duba da irin matakan da ake ɗauka don magance ƙalubalen
  • Ya yabawa shugaban ƙasa Tinubu kan yadda yake ƙoƙari da jajircewa wajen ganin rayuwar ƴan Najeriya ta inganta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Ganduje, ya ce nan ba da dadewa ba Najeriya za ta shawo kan ƙalubalen da ta ke fuskanta.

Ganduje ya bayyana cewa hakan zai faru ne idan aka yi duba da irin matakan da ake ɗauka na baya-bayan nan, don shawo kan matsalolin, cewar rahoton jaridar Vanguard.

Kara karanta wannan

Daga tono badaƙalar N3.5bn, ma'ajiyin kuɗin jam'iyyar adawa ta ƙasa ta shiga babbar matsala

Ganduje ya ce sauki na tafe
Ganduje ya bukaci 'yan Najeriya su kara hakuri Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Dr Abdullahi Umar Ganduje - OFR
Asali: Facebook

Ganduje ya bayyana haka ne a lokacin da ya karɓi bakuncin masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC na yankin Arewa ta tsakiya a Abuja, rahoton jaridar The Guardian ya tabbatar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me Ganduje ya ce kan halin da ake ciki?

Shugaban jam'iyyar ya bayyana cewa suna sane da irin maganganun da ƴan adawa suke yi kan halin da ake ciki a ƙasar nan, amma hakan ba zai sanya su ƙi yin abin da ya dace ba.

A kalamansa:

"Mun san cewa suna ci gaba da sukar shugaban ƙasa kan ƙalubalen da ƴan Najeriya ke fuskanta, mun yi amanna cewa nan ba da jimawa ba matsalolin nan za su zo ƙarshe.
"Dole ne mu gode wa shugaban ƙasa kan shirinsa na sabunta fata, ƙoƙarinsa, da jajircewarsa, kuma muna tabbatar masa da cewa muna gare shi ɗari bisa ɗari."

Kara karanta wannan

"Ba a kyauta mana": Soja ya fusata kan kyautar da Tinubu ya yi wa 'yan wasan Suoer Eagles

Ganduje ya samu yabo

Tun da farko, Sanata Ameh Ebute, tsohon shugaban majalisar dattawa da ya jagoranci tawagar, ya ce sun kai ziyarar ne domin nuna godiya ga Ganduje kan salon shugabancinsa.

Ya kuma ce ziyarar ta zo ne domin ƙarfafa masa gwiwar ci gaba da yi wa jam’iyyar APC aiki a matsayin shugabanta na kasa.

Ebute ya ce ba su da masaniya kan yunƙurin da wasu mutane a yankin Arewa ta tsakiya, suke yi na ganin shugabancin jam'iyyar na ƙasa ya koma yankin.

Gwamnatin Tinubu Za Ta Marasa Ƙarfi Tallafi

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta shirya raba tallafin kayan abinci ga ƴan Najeriya marasa ƙarfi.

Ministan noma, Abubakar Kyari, wanda ya bayyana hakan ya ce za a raba kayayyakin ne kyauta domin tsamo mutane daga halin yunwar da ake ciki a ƙasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel