Tsadar Rayuwa: Gwamnatin Tinubu Ta Jawo ’Yan Najeriya Na Mutuwa Saboda Yunwa, in Ji Hadimin Atiku

Tsadar Rayuwa: Gwamnatin Tinubu Ta Jawo ’Yan Najeriya Na Mutuwa Saboda Yunwa, in Ji Hadimin Atiku

  • Mai magana da yawun, Atiku Abubakar, ya ce gwamnatin Tinubu ya jefa 'yan Najeriya cikin tsaka mai wuya ta hanyar jawo tsadar rayuwa
  • Mr Phrank Shaibu ya yi ikirarin cewa Tinubu ya shirya jefa Najeriya cikin yunwa, talauci da kuncin rayuwa tun kafin ya hau mulki
  • Shaibu ya kuma yi nuni da cewa har yanzu babu wani yunkuri da gwamnatin ke yi na daidaita lamuran kasar sai dora wa Buhari laifi da take yi

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Mai magana da yawun tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, Phrank Shaibu, ya yi gargadin cewa ‘yan Najeriya na mutuwa daga munanan manufofin gwamnatin shugaba Bola Tinubu.

A wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, ya yi takaicin cewa har yanzu babu wani yunkuri na dakile tashe tashen hankula da tsadar rayuwa da ake fama da su a kasar.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Sarkin Musulmi ya fadi masifar da za ta faru idan ba a dauki mataki ba, akwai dalilai

Hadimin Atiku ya zargin Tinubu da kuntatawa talaka da lalata tattalin arziki.
Hadimin Atiku ya zargin Tinubu da kuntatawa talaka da lalata tattalin arziki. Hoto: @PBATMediaCentre
Asali: Facebook

Phrank Shaibu, ya yi zargin cewa yunwa, talauci, da kunci irin wanda ba a taba ganin irinsa ba na daga cikin tanadin da Tinubu ya yi wa 'yan Najeriya tun kafin ya hau mulki, in ji Tribune Online.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shaibu ya caccaki Shugaba Bola Tinubu

Ya ce:

“Tinubu kamar likitan boge ne da ke ƙoƙarin warkar da mai ciwon daji. Amma likitan boge zai iya kashe majiyyacin da sauri fiye da ita kanta cutar, to kamar haka take faruwa a Najeriya."

Shaibu ya ce maimakon Tinubu ya kama aiki tukuru, sai buge da zargin magabacinsa, shugaba Buhari, da laifin damka masa baitul mali da ba kudi a ciki, da sauran zantuka marasa tushe.

"Ya kuma manta cewa manufofinsa masu kama da 'kabukabu' ne suka jawo tabarbarewar tattalin arziki da kuma jawo dimbin zanga-zanga a fadin kasar nan”.

Kara karanta wannan

Tsadar Rayuwa: An bukaci Shugaba Tinubu ya gaggauta yin murabus, karin bayani ya bayyana

- A cewar Shaibu

Illolin manufofin gwamnatin Tinubu ga 'yan Najeriya - Shaibu

A mahangar Shaibu, a karkashin kulawar Tinubu, talauci ya kai kololuwa, inda ma'aunin hauhawar farashin abinci ya kai kaso 33.

Ya yi nuni da cewa, illar mnaufofin Tinubu zai haifar da rashin aikin yi, karuwar masu daukar ransu, karuwar aikata laifuka da kuma karuwar yawan yaran da ba sa zuwa makaranta.

Shaibu ya yi nuni da cewa asibitin kula da masu tabin hankali na tarayya da ke Legas, ya nuna cewa asibitin ya samu karin kaso 100 a yawan masu tabin hankali da aka kwantar a asibitin.

Tsadar rayuwa: Tinubu ya sa a kama masu boye kayan abinci

A wani labarin, Legit Hausa ta ruwaito cewa shugaba Tinubu ya gana da gwamnoni da shugabannin tsaro a yau Alhamis a Abuja.

A yayin ganawar, Tinubu ya ba jami'an tsaro umarnin hada kai da gwamnoni don kama masu boye kayan abinci a Najeriya

Asali: Legit.ng

Online view pixel