Naira Ta Sake Faduwa Ƙasa, Darajar Dala Ta Cigaba da Tashi Zuwa N1600 a Kasuwar Hada-Hadar Kudi

Naira Ta Sake Faduwa Ƙasa, Darajar Dala Ta Cigaba da Tashi Zuwa N1600 a Kasuwar Hada-Hadar Kudi

  • A yayin da aka zura ido aga tasirin matakan da gwamnati ta dauka na daidaita darajar Naira, a hannu daya darajar kudin ta kara faduwa
  • A safiyar ranar Alhamis, darajar dala ta kai N1,600 a kasuwar hada-hadar kudi ta duniya, wanda ya saba da farashinta na jiya Laraba
  • A jiya Laraba an yi hada-hadar kudin ne akan NN1,503.38 kowacce dala 1, wanda ya haura N1,499.07 da aka kasuwancinta a ranar Talata

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Naira ta fadi zuwa N1,600 idan aka kwatanta da dala a ranar Alhamis yayin da tattalin arzikin Najeriya ke ci gaba da tabarbarewa a karkashin Shugaba Bola Tinubu.

A cewar shafin hada-hadar kudi na Aboki, Naira ta fadi kasa zuwa Naira 1,600 akan kowacce dala 1 duk da kokarin da babban bankin Najeriya ya yi na ceto faduwar Nairar.

Kara karanta wannan

Gombe: Tashin hankali yayin da mummunar gobara ta ɓarke a barikin 'yan sanda, bayanai sun fito

Darajar Naira na kara tabarbarewa a kasuwar hada-hadar kudi, yanzu ta koma N1,600
Darajar Naira na kara tabarbarewa a kasuwar hada-hadar kudi, yanzu ta koma N1,600
Asali: Getty Images

Duk da cewa Naira ta sha faduwa a kan dala kafin Tinubu ya hau karagar mulki, sai dai faduwar kudin ta kara ta'azzara sakamakon karya darajarta da gwamnati ta yi sau biyu a watanni takwas.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda aka yi hada-hadar Naira zuwa Dala a jiya da yau

Bayanai daga kasuwar hada-hada ta FMDQ sun nuna cewa ana cinikin dala a kan N1,503.38 a ranar Laraba, idan aka kwatanta da N1,499.07 a ranar Talata, Business Day ta ruwaito.

An rufe kasuwar a kan N1,582 kan kowace dala a ranar Laraba, wanda ke nuna faduwar kudin da aka samu idan aka kwatanta da yadda aka rufe N1,550 kan kowace dala ranar Talata.

A kasuwar bayan fage kuwa, ana musayar Naira da dala akan farashin da ya kai N1,533/$1 zuwa N1,590/$1 a ranar Laraba, yayin da ta kai N1600/$1 a ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

Tsohon gwamna a Arewa ya tona asirin wadanda ke da hannu a faduwar darajar Naira

Tsare-tsaren gwamnati sun jawo faduwar Naira

Tsare-tsaren kudi na gwamnatin Tinubu, a mahangar Peaoples Gazette sun taka rawar gani sosai wajen faduwar darajar Naira bayan da ya karya darajarta.

Manufar tattalin arzikin Tinubu ta fara ne ta hanyar soke tallafin man fetur da rugujewar kasuwannin hada-hada hanyar hade su waje daya a tsarin 'I$E'.

Wannan tsarin ya yi matukar karya darajar Naira da kashi 98 cikin 100, in ji wani rahoto na Price Water Coopers.

Ci gaba da faɗuwar darajar Naira, na daga abubuwan da ke ci wa gwamnati tuwa a kwarya tare da zama babban ƙalubale ga Shugaba Bola Tinubu.

Faduwar Naira ya jefa kamfanoni 3 sun tafka asara a Najeriya

A bangare daya kuma, Legit Hausa ta ruwaito yadda wasu manyan kamfanonin Najeriya guda 3 suka tafka asarar naira biliyan 140 a lokaci daya.

Rahotanni sun bayyana cewa Kamfanin BUA, Flourmills, Cadbury Plc, sun tafka wannan asarar ne biyo bayan faduwar darajar Naira da karya darajar ta da gwamnati ta yi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel