Kamar Man Fetur, Gwamnatin Najeriya Za Ta Janye Tallafin Wutar Lantarki

Kamar Man Fetur, Gwamnatin Najeriya Za Ta Janye Tallafin Wutar Lantarki

  • Yayin da 'yan Najeriya ke kokawa kan cire tallafin man fetur, gwamnatin Shugaban kasa Bola Tinubu tana shirin daukar sabon mataki a bangaren wutar lantarki
  • Ministan wutar lantarki, Adebayo Adelabu, ya bayyana cewa Najeriya ba za ta iya ci gaba da biyan tallafin wutar lantarki ba
  • Adelabu ya ce hakan ya samo asali ne sakamakon basussukan da kamfanonin samar da wutar lantarki ke bin kasar

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Ministan wutar lantarki, Adebayo Adelabu, ya ce Najeriya ba za ta iya ci gaba da bayar da tallafin wutar lantarki ba, inda ya ce kasar na bukatar fara aiwatar da tsari na daban mai inganci.

Ya ce hakan ya faru ne saboda basussukan da kamfanonin samar da wutar lantarki (Gencos) da na iskar gas ke bin kasar, rahoton The Nation.

Kara karanta wannan

Fitaccen malami ya yi hasashen sabon farashin naira kan dala, ya ce buhun shinkafa zai kai 90k

A cewarsa kamfanonin samar da wutar lantarki na bin kasar naira tiriliyan 1.3 yayin da kamfanonin gas ke bin dala biliyan 1.3.

Gwambatin Najeriya za ta janye tallafin lantarki
Kamar Man Fetur, Gwamnatin Najeriya Za Ta Janye Tallafin Wutar Lantarki Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Adelabu ya bayyana hakan ne a wata zantawa da ya yi da manema labarai a babban birnin tarayya Abuja a ranar Laraba, 14 ga watan Fabrairu.

Su wa za a damkawa ragamar raba wuta?

Ministan ya bayyana cewa naira biliyan 450 kacal aka ware na tallafin lantarki a bana, amma kuma ma'aikatar na bukatar sama da naira tiriliyan biyu don tallafin.

Ya ce za a bar gwamnatocin jihohi su rika samar da wutar lantarki da kansu don samar da wutar lantarki ga jihohinsu.

Ya yi ikirarin cewa dalilan da suka haddasa faduwar babban layin wuta sau shida a wasu yankunan arewa maso gabashin kasar tun daga Disambar 2023 sun hada da karancin iskar gas, tsufar kayan aiki da sauransu.

Kara karanta wannan

Adam Zango ya bayyana lalurar da ta same shi bayan rabuwa da matarsa

A cewarsa, kamfanin raba wutar lantarki ta TCN yana da ayyuka sama da 100 da ba a kammala ba saboda bambance-bambancen alkaluman kwangilolin da ke haifar da hauhawar farashin kayayyaki.

Kan haka ne yace kamfanin ba zai fitar da wasu sabbin kwangiloli ba har sai an kammala dukkan ayyukan.

Ministan ya kara da cewa kasafin 2024 yana da sama da naira biliyan 50 da aka ware domin gina kananan layuka da za su samar da wutar lantarki a yankunan karkara, rahoton Channels TV.

Tashar wuta ta samu tangarda

A wani labarin, mun ji a baya cewa jihohi akalla hudu ba su da wutan lantarki a daidai lokacin da mu ke tattara rahoton nan a ranar Lahadi.

Jihohin Najeriyan da abin ya shafa kamar yadda muka fahimta su ne: Kaduna, Sokoto, Zamfara, sai kuma jihar Kebbi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel