Bola Tinubu
Jigon jam'iyyar APC ya shawarci Bola Tinubu kan abin da ya kamata ya yi kan masu daga tutucin Rasha yayin da ake cigaba da zanga-zangar tsadar rayuwa a kasar.
Babban malamin addinin Musulunci a Najeriya, Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi ya ba shugaba Bola Tinubu shawarin dawo da tallafin man fetur a Najeriya.
Tsohon shugaban cibiyar harkokin ƙasashen waje (NIIA), Farfesa Bola Akinterinwa ya bayyana cewa matasan da ke daga tutar Rasha ba 'yan Najeriya ba ne.
Gwamnatin Tarayya ta shirya fara siyar da shinkafar N40,000 mai nauyin 50kg a Najeriya ga ma'aikatan gwamnati domin ragewa al'umma halin da suke ciki.
Jam'iyyar PDP ta dakatar da tsohon gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom kan wasu zarge-zarge da dama da suka hada da cin dunduniyarta da kawo rudani.
Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya umarci hafsoshin tsaro su kawo ƙarshen ɗaga tutocin Rasha da masu zanga zanga suke yi a wasu jihohin Arewacin Najeriya.
Bola Tinubu ya sha suka kan jawabin da ya gudanar a jiya Lahadi 4 ga watan Agustan 2024 inda suka ce bai yi magana kan bukatun masu zanga-zanga ba.
Shugaban Jami'ar Al-Istiqama da ke Kano, Farfesa Salisu Shehu ya bayyana yadda suka jagoranci zanga zanga tare da Sheikh Jafar amma ta dawo tarzoma a Kano.
Tun fara zanga zangar adawa da tsadar rayuwa a Najeriya an samu muhimman abubuwa da suka ja hankalin al'umma wanda suka hada da daga tutar Rasha da jawabin Tinubu.
Bola Tinubu
Samu kari